Aminiya:
2025-04-04@10:20:48 GMT

Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba

Published: 3rd, April 2025 GMT

Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba.

Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya.

Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato

Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar.

Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas ne ya bayar da kwangilar sake gina gadar a watan da ya gabata amma har yanzu ba a kai ga kwangilar zuwa wurin ba.

Masu ababen hawa da ke bin hanyar Jalingo da Wukari, an tilasta musu karkata zuwa hanyar garin Garba-Chede da ke ƙaramar hukumar Bali domin ci gaba da tafiya.

Masu ababen hawa da suka maƙale a ranar Laraba sun bayyana rashin jin daɗinsu kan gazawar gwamnatin tarayya na sake gina gadar kafin damina ta fara.

Wani direban babbar mota mai suna Bello Adamu ya ce direbobi da masu ababen hawa ba su ji daɗin yadda ba a sake gina gadar cikin lokaci mai kyau ba, kuma yanzu damina ta fara kawar da gadar wucin gadi a madadin babbar gadar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Taraba Wukari ababen hawa da

এছাড়াও পড়ুন:

Turji ya kusa komawa ga mahallici –  Sojoji

A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Nijeriya ta ce ana cigaba da farautar  ƙasurgumin ɗanbindiga, Kachalla Bello Turji wanda sojojin ƙasar suka daɗe suna nema ya kusa komawa ga mahalicci.

Rundunar ta bayyana cewa kuma kwanakinsa sun kusa ƙarewa.

Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta miƙa Janar Tsiga da wasu ga NSA Gobara ta tashi a Jami’ar Northwest da ke Kano

Ta kuma yi watsi da iƙirarin da ake na cewa sojoji sun rage kai hare-hare kan makiyaya, ’yan bindiga, ɓarayin shanu da sauransu, inda ta ƙara da cewa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen kame Turji.

Wannan na zuwa ne kimanin kwana ɗaya bayan Turji ya kashe manoma 11 a garin Lugu da ke ƙaramar Isa ta Jihar Sokoto

An samu rahoton Turji yana dawowa ne daga ziyarar Sallah da ya kai wata unguwa a Isa, lokacin da ya kai harin.

Da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a hedikwatar tsaro a yayin ganawa da manema labarai, daraktan watsa labaran na rundunar tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Markus Kangye, ya ce za su iya ci gaba da farauta tare da ganin bayan manyan ’yan bindiga da ke cikin dazukan ƙasar nan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila ta sake kai hare-hare ta sama kan kasar Siriya
  • Xi Ya Jaddada Hada Karfi Da Karfe Wajen Gina Kyakkyawar Kasar Sin 
  • Turji ya kusa komawa ga mahallici –  Sojoji
  • Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato
  • Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang
  • Janar Tsiga Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Bayan Shafe Kwanaki 56 A Hannun ‘Yan Bindiga 
  • Babban daraktan hukumar IAEA, Rafael Grossi, zai ziyarci Iran cikin makwanni masu zuwa
  • Mamakon Ruwan Sama: Matafiya sun Maƙale a Taraba Sakamakon Ɓallewar Gada
  • Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci