‘Yan Bindiga A Ƙarƙashin Jagorancin Turji Sun Kashe Manoma 12 A Sokoto
Published: 3rd, April 2025 GMT
Ya ce, “Akwai rahoton cewa Turji ya shirya zai ziyarci yankin Gabashin Gatawa domin gudanar da bukukuwan Sallah, amma matakin da jama’a suka dauka na sanar da jami’an tsaro ya dakatar da shi ga hakan.
“Wannan na iya zama dalilin da ya sa Bello Turji ya huce fushinsa a kan manoman da ba su ji ba gani ba.
Sai dai hukumomin ‘yansanda a jihar sun ki cewa komai kan lamarin.
Majiyar ‘yansandan ta yi ikirarin cewa, “tunda ana ci gaba da aikin hadin gwiwa na sojoji a yankin, ‘yansanda ba su da hurumin yin magana kan ci gaban tsaro a yankin.
Da aka tuntubi runduna ta 8 ta sojojin Nijeriya ta mika wakilinmu ga rundunar ‘Operation FASAN YAMMA’, wanda har yanzu bai amsa bukatar wakilinmu ba kan bukatar tabbatar da lamarin harin har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sahel: CILSS ta yi gargadi game da sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin sahel
Kwamitin kasa da kasa kan yaki da fari a yankin Sahel (CILSS) ya yi wani gargadi na musamman kan sake bullar ‘’kwarin dango’’ a yankin Sahel, wanda ke da hadarin yin illa nan gaba.
Shafin yanar gizo na CILSS ya bayar da rahoton cewa, “Kwananan kwararru kan yaki da fari sun fitar da sanarwar sake bullar farar kwarin dango a kasashen Sahel da dama.”
CILSS ta yi gargadin cewa “, wannan na iya haddasa matsala sosai a lokacin noma a yankin da ya riga ya kasance mai rauni’’.
Yayin da ake fuskantar wannan barazana, CILSS na ganin cewa, ya zama wajibi a ba da goyon baya mai dorewa ga kasashendake sahun gaba wajen fuskantar irin wannan matsala na yankin Sahel, wajen aiwatar da shirye-shiryensu na gaggawa, domin dakile duk wata matsalar fari da ka iya yin illa ga kakar noma mai zuwa a yankin Sahel.