Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka.

A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kira ga duniya da ta bayyana goyon bayanta ga al’ummar Palasdinu ta hanyar daukar matakan gaggawa da suka hada da dukkanin hanyoyin soja, tattalin arziki, da diflomasiyya mai  inganci.

Dangane da haka ne kungiyar ta yi kira ga limaman masallatan Juma’a a fadin duniya da su sadaukar da hudubar sallar Juma’a na gobe don magana kan wajabcin magance wahalhalu da radadin al’ummar Palastinu da kuma bukatar kawo karshen kisan gillar da gwamnatin sahyoniya ta ke yi wa Palastinawa.

Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta jaddada a cikin wannan bayani cewa, wannan cibiyar ta bibiyi matukar damuwa da bakin ciki da kisan gilla, da laifukan yaki , da yunwa da kishirwa, da kuma gudun hijira da gwamnatin yahudawan sahyoniya tare da goyon bayan ma’abota girman kan duniya suka saka mazauna Gaza a ciki.

Kungiyar ta kuma yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin bil adama da su ci gaba da tallafawa Gaza da kuma tattara laifukan da ake aikatawa har sai an dakatar da harin, da kuma tabbatar da adalci. Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta kuma yi kira da a gudanar da jerin gwano na lumana bayan sallar Juma’a a gobe a dukkanin kasashen musulmi, domin bayyana goyon bayansu ga zirin Gaza da kuma yin Allawadai da ayyukan wuce gona da irin Isra’ila.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta

এছাড়াও পড়ুন:

 Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza

A yau Laraba sa jijjifin Safiya an sami shahidai 3 a Gaza da hakan ya kara yawan shahidai zuwa 40 a cikin sa’o’i 24.

Bugu da kari, baya ga shahidan da suke faduwa a kowace rana, ana fama da matsananciyar yunwa a cikin yankin, bayan karewar kayan abincin HKI ta sake komawa yaki kwanaki 44 da su ka gabata.

A cikin sansanin ‘yan hijira na “Nusairat”  mutane 3 sun yi shahada da su ka hada da karamar yarinya sanadiyyar harin da sojojin na HKI su ka kai wa yankin.

A gabashin birnin Khan-Yunus ma dai wasu Falasdinawa sun yi shahada.

Daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun wuce 52,000,wadanda su ka jikkata kuma sun haura 100,000.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban INEC Ya Yi Kira Da A Sake Fasalin Tsarin Zabe Gabanin 2027
  • Yunwa Ta Kazanta A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Tun Bayan Da Majalisar Dinkin Duniya Ta Dakatar Da Ayyukanta
  • Ministan Tsaron Iran Ya Bayyana Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya A Matsayar Alamar Yan Ta’adda
  • Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Jaddada Goyon Baynata Ga Kungiyar Hizbullahi Ta Kasar Lebanon
  • WHO, ta nuna kaduwa da abin da ke faruwa a Gaza
  • Gwamnatin Kano Zata Kashe Naira Miliyan Dubu 51 Don Aiwatar Da Ayukka
  • Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko 
  • An kashe Falasdinawa kusan 30 a wani sabon kisan kiyashin Isra’ila a Gaza
  •  Manyan Malaman Roman Katolika Sun Fara Taron Zabar Paparoma
  •  Falasdinawa 40 Sun Yi Shahada A Cikin Sa’oi 24 A Gaza