Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Gyara Kuskurenta Na “Kakaba Haraji Ramuwar Gayya”
Published: 3rd, April 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna.
Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar Sin da sauran kasashe, wanda hakan ya sabawa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya da matukar yin illa ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kana ya nanata cewa, babu wanda zai yi nasara a takaddamar cinikayya ko harajin fito, kuma kariyar cinikayya ba za ta samar da mafita ba.
A wani ci gaban kuma, kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin He Yadong ya bayyana a taron manema labaru na yau Alhamis cewa, kasar Sin a shirye take ta warware damuwar da ke tsakaninta da Amurka ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito da tuntubar juna. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Trump na shan martani game da harajin da ya laftawa kasashen duniya
Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini tare da shan alwashin ramuwar gayya game da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta musu kankan kayayyakin da ake shigowa da su kasar.
Gwamnatoci da kamfanoni da dama sun sanar da matakan gaggawa na samar da matakan dakile matakin da Amurkan ta dauka kansu.
A ranar Laraba ne, ya sanya harajin kan duk kayayyakin da ake shigowa da su Amurka da kuma karin haraji kan wasu manyan abokan kasuwancin kasar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga kamfanonin Turai da su dakatar da shirin zuba jari a Amurka.
“Ina ganin abin da ke da muhimmanci, shi ne a dakatar da saka hannun jarin da za a cikin ‘yan makonnin nan har sai an fayyace al’amura da Amurka,” in ji Macron yayin ganawarsa da wakilan masana’antun Faransa.
Kasar China ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya ta sha alwashin daukar fansa kan harajin kashi 54% na Trump kan shigo da kaya.
Hakazalika, Tarayyar Turai ta sanar da cewa za ta bullo da matakan da za su bijirewa aikin da Amurka ke yi na kashi 20%.,” in ji shugabar EU Ursula von der Leyen.
Koriya ta Kudu, Mexico, Indiya, da sauran abokan cinikin Amurka da yawa sun ce za su daina aiki a yanzu yayin da suke neman rangwame kafin harajin da aka yi niyya ya fara aiki a ranar 9 ga Afrilu.
Jami’an Mexico sun ce za su ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Trump, yayin da
Canada ta ce tana bukatar yin garambawul ga tattalin arzikinta domin rage dogaro da Amurka, ta kuma sha alwashin mayar da martani kan harajin da Trump ya saka mata.