Xi Ya Jaddada Hada Karfi Da Karfe Wajen Gina Kyakkyawar Kasar Sin
Published: 4th, April 2025 GMT
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da hada karfi da karfe wajen gina kyakkyawar kasar Sin, da kuma sa kasar ta kara zama kore shar ta hanyar dasa itatuwa.
Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojan kasar, ya bayyana hakan ne yayin da yake halartar aikin sa kai na dashen itatuwa a nan birnin Beijing a yau Alhamis.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Jaddada Matsayinta Kan Batun Tace Sinadarin Yuranium A Batun Tattaunawa Da Amurka
Jamuhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada matsayinta kan batun tace sinadarin yuraniyo.
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatemeh Mohajerani ta bayyana cewa, Iran na kokarin yin shawarwari ne domin samar da amana da samar da gaskiya game da shirinta na nukiliya domin dage takunkumi kanta.
A cikin taron manema labarai na mako-mako da ta gudanar a jiya litinin, Mohajerani ta mayar da martani ga wata tambaya game da tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, inda ta ce, shin bangarorin biyu sun cimma matsaya dangane da kasar da za a aike da hajojin uranium da Iran ta inganta? Shin Iran ta amince ta mika wadannan haja zuwa Rasha? Ta ce: Ina so in bayyana dangane da kashi na farko na tambayar cewa wasu daga cikin wadannan lamurra jajayen layukan Iran ne.
Wasu batutuwa a bude suke don tattaunawa, amma, kamar yadda aka ambata a baya, wasu daga cikin abubuwan da ake tattaunawa a kafafen yada labarai sun fada cikin jajayen layin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne, dangane da kasar Rasha, tana jaddada cewa, a matsayinta na mamba na dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya tana da matukar muhimmanci a wurin Iran, kuma hadin gwiwar kut-da-kut da ke tsakanin Iran da Rasha, ya bai wa kasar Rasha rawar da ta taka wajen yin shawarwarin.