NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta
Published: 4th, April 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Akwai cututtuka da dama da ke yaɗuwa, kuma mafi yawan mutane da ke ɗauke da su, ba su san suna da su ba.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce zaman lafiya, samun abinci da wadata, da rashin damuwa a ƙwaƙwalwa na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da lafiyar mutum.
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika AlƙawariƊaya daga cikin manyan cututtukan da ke damun mutane da yawa, ita ce cutar hawan jini.
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi bayani ne kan cutar hawan jini da kuma hanyoyin da za a bi don magance ta.
Domin sauke shirin, latsa: nanhttps://www.buzzsprout.com/1822045/episodes/16913858-dalilan-kamuwa-da-cutar-hawan-jini-da-hanyoyin-magance-ta.mp3?download=true
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Bayani Hawan Jini lafiya Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙarin ’yan Najeriya za su fuskanci talauci nan da 2027 — Bankin Duniya
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa talauci a Najeriya zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari a cikin shekaru biyar masu zuwa, ciki har da shekarar zaɓe ta 2027.
Wannan hasashe yana ƙunshe ne a cikin rahoton Bankin wanda aka fitar a lokacin taron bazara na Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da ake yi a birnin Washington, D.C., a ƙasar Amurka.
Rahoton ya jaddada cewa duk da wasu nasarorin da aka samu a harkokin tattalin arziki a kwanakin baya, musamman a ɓangaren da ba na man fetur ba a cikin rubu’i na ƙarshe na shekarar 2024, matsalolin da suka shafi dogaro da albarkatun ƙasa da kuma raunin ƙasa na iya kawo cikas ga ci gaba.
A cewar Bankin Duniya, Najeriya, tare da wasu ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni a yankin kudu da Sahara, za su fuskanci ƙaruwar talauci —saɓanin ƙasashen marasa arzikin albarkatu, waɗanda ake tsammanin za su samu raguwar talauci cikin sauri.
’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa NAJERIYA A YAU: Dalilin da zazzaɓin cizon sauro ba ya jin maganiRahoton ya bayyana cewa, “Ana hasashen talauci zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari tsakanin 2022 zuwa 2027a ƙasashe masu arzikin albarkatu da masu rauni—ciki har da manyan masu tattalin arziƙo kamar Najeriya da Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.”
A halin da ake ciki, Sanatan da ke wakiltar Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, ya yi kira ga ƙasashen a Afirka, Bankin Duniya, da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da su ba da fifiko ga amfani da bayanai don ci gaban Afirka.
Da yake magana a yayin taron bazara na IMF/Bankin Duniya a Washington, D.C., Amurka, Sanata Jimoh Ibrahim ya jaddada muhimmancin bayanai a ci gaban tattalin arziki da siyasa.
Ya ce, “Idan babu bayanai ba, babu wanda zai iya rage aikata laifuka yadda ya kamata ko kuma gudanar da gwamnatin da ke da nufin cimma nasarar rage talauci.”
Ya ƙara da cewa, “Bayanai kan yawan jama’a da cikakkun bayanai na mutane sun nuna cewa ya kamata ’yan ƙasa su mallaki fasfo na tantancewa domin tattara muhimman bayanai game da su wane ne su da kuma abin da suke yi.”
Sanatan ya yi gargadi ga IMF game da yin hasashe ba tare da ingantattun bayanai ba, yana mai cewa irin waɗannan hanyoyin ba su da inganci.