HausaTv:
2025-04-04@23:44:14 GMT

Kisan ma’aikatan ceto : MDD ta gargadi Isra’ila game da aikata laifin yaki

Published: 4th, April 2025 GMT

Kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi Isra’ila game da harin da ya yi sanadin mutuwar ma’aikatan ceto a Gaza yana mai cewa hakan zai iya kasancewa ‘lafin yaki’. Ma’aikatan agaji 15 ne suka ras arayukan a wani kazamin hari da Isra’ila ta kai kan motocin daukar marasa lafiya a Gaza wada ya fiddo a fili irin ” laifuffukan yaki da sojojin Isra’ila suka kwashe tsawon lokaci suna aikatawa a zirin Gaza”.

Kafin hakan dama hukumar kula da hakkin bil adama ta MDD ta amince da kudurin dake kira ga Isra’ila da kada ta aikata kisan kiyashi a zirin Gaza.

An amince da kudurin ne ranar Laraba yayin taron hukumar na 58, bayan ya samu kuri’un amincewa 27 da na kin amincewa 4, kana kasashe 16 sun kaurace wa kada kuri’ar.

Kudurin ya kuma bayyana takaici game da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Isra’ila ta yi, tare da yin kira da ta sauke nauyin dake wuyanta.  

Har ila yau, kudurin ya soki yadda Isra’ila ta yi amfani da yunwa a matsayin wata dabara ta yaki a Gaza, da hana samar da agajin jin kai da kawo tsaiko ga samar da kayayyakin agaji da hana fararen hula abubuwan da suke bukata na rayuwa, kamar abinci da ruwa da lantarki da makamashi da hanyoyin sadarwa.

Ya kuma bayyana damuwa matuka game da kalaman jami’an Isra’ila da ka iya ingiza kisan kiyashi, inda ya bukaci Isra’ila ta sauke nauyin dake wuyanta bisa doka na kare aukuwar kisan kiyashi.

Bugu da kari, kudurin ya gabatar da wasu jerin bukatu ga Isra’ila, ciki har da tabbatar da samar da agajin jin kai ba tare da tangarda ba da gaggauta dawo da tsarin samar da muhimman kayayyakin bukata ga Palasdinawa a Gaza da ba Palasdinawan da suka rasa matsugunansu damar komawa dukkan yankunan zirin Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman da makamai masu linzami

Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama.

Kakakin Rundunar sojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree ya tabbatar da cewa, sojojin Yaman sun gudanar da wani shiri na soji na hadin gwiwa, inda suka yi arangama da jirgin ruwan Amurka Harry Truman da jiragen yakin da yake dauke da su  a arewacin tekun Bahar Maliya.

Saree ya ci gaba da cewa, a harin an yi amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka, kuma harin ya cimma nasara kamar yadda aka tsara, inda ya ce an dauki tsawon sa’o’i da dama ana gudanar da farmakin, kamar yadda kuma a lokaci guda sojojin Yeman sun dakile wani bangare na harin Amurka.

Ya kuma kara tabbatar da cewa dakarun na Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan dukkanin jiragen ruwan yakin Amurka da kuma jiragen da suka keta dokar hana shiga yankunan da aka ayyana, yana mai bayyana cewa wadannan hare-haren wuce gona da iri na Amurka ba za su hana su cika alkawarin da suka dauka na tallafawa al’ummar Palasdinu ba.

Saree ya tabbatar da cewa sojojin Yeman na ci gaba da gudanar da ayyukansu a cikin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, kuma ba za su gushe ba har sai an dakatar da kai farmaki a kan Gaza tare da kawo karshen killacewar da ake yi wa al’ummar yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ina Mafita Game Da Ƙalubalen Ƙarancin Abinci A Nijeriya
  • Ana Zargin Wani Ɗansanda Da Kisan Wata Mata Kan Cin Hancin Naira 2,000 — Bincike
  • Isra’ila ta sake kai hare-hare ta sama kan kasar Siriya
  • Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman da makamai masu linzami
  • Kungiyar Malaman Musulmi ta yi kira da a dakatar da kisan kiyashi a Gaza cikin gaggawa
  • Isra’ila na karbe yankuna a zirin Gaza
  • ‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga, Sun Ceto Ɗalibai 2 A Nasarawa
  • Kisan Mafarauta: Babu wanda aka kai wa harin ramuwar gayya a Kano — Ƙungiyoyin Matasa
  • Sojojin Yemen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kataparen Jirgin Ruwan Yaki Mai Daukar Jirage Na kasar Amurka