HausaTv:
2025-04-04@23:53:43 GMT

Iran ta yi kira ga kungiyar Shanghai ta yi Allah wadai da barazanar Trump

Published: 4th, April 2025 GMT

Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar.

A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari.

Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta  dokokin kasa da kasa, da kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya wanda ya haramta amfani da karfi karara a kan iyakokin kasa da ‘yancin kai.

Takht Ravanchi ya bayyana cewa Iran ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya yi Allah wadai da wannan hali da ba za a amince da shi ba tare da daukar matakan da suka dace don kiyaye zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.

Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya sake jaddada matsayar kasar Iran da cewa duk wani yunkuri daga Amurka zai fuskanci mai da martani cikin gaggawa.

Ya yi kira da a fitar da sanarwar hadin gwiwa ta SCO da ke yin Allah wadai da barazanar Amurka tare da yin kira ga kwamitin sulhun da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: yi Allah wadai da

এছাড়াও পড়ুন:

Allah Ya Yi Wa Galadiman Kano, Abbas Sanusi, Rasuwa 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sayyid Husi: Hare-haren Amurka Ba Za Su Yi Tasiri Akan Karfinmu Ba
  • Shugaban Kasar Iran Ya Fadawa Muhammad Bin Salman Kan Cewa Tehran Tana Shirin Kare Kanta
  • Rasha ta gargadi Amurka kan duk wani gigin ka wa kasar Iran hari
  • Kungiyar Malaman Musulmi ta yi kira da a dakatar da kisan kiyashi a Gaza cikin gaggawa
  •  Kasar Afirka Ta Kudu Tana Ci Gaba Da Bibiyar “Isra’ila” A Kotun Duniya Ta Manyan Laifuka
  • Babban daraktan hukumar IAEA, Rafael Grossi, zai ziyarci Iran cikin makwanni masu zuwa
  • Araghchi : Iran a shirye take don tattaunawa amma barazanar soji daga Amurka na dagula yanayin’
  • Iran Ta Bukaci Hukumar IAEA Ta Bayyana Matsayinta A Shirin Makamashin Nukliya Na Kasar
  • Allah Ya Yi Wa Galadiman Kano, Abbas Sanusi, Rasuwa