HausaTv:
2025-04-25@08:35:58 GMT

Trump na shan martani game da harajin da ya laftawa kasashen duniya

Published: 4th, April 2025 GMT

Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini tare da shan alwashin ramuwar gayya game da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta musu kankan kayayyakin da ake shigowa da su kasar.

 Gwamnatoci da kamfanoni da dama sun sanar da matakan gaggawa na samar da matakan dakile matakin da Amurkan ta dauka kansu.

A ranar Laraba ne, ya sanya harajin kan duk kayayyakin da ake shigowa da su Amurka da kuma karin haraji kan wasu manyan abokan kasuwancin kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga kamfanonin Turai da su dakatar da shirin zuba jari a Amurka.

“Ina ganin abin da ke da muhimmanci, shi ne a dakatar da saka hannun jarin da za a cikin ‘yan makonnin nan har sai an fayyace al’amura da Amurka,” in ji Macron yayin ganawarsa da wakilan masana’antun Faransa.

Kasar China ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya ta sha alwashin daukar fansa kan harajin kashi 54% na Trump kan shigo da kaya.

Hakazalika, Tarayyar Turai ta sanar da cewa za ta bullo da matakan da za su bijirewa aikin da Amurka ke yi na kashi 20%.,” in ji shugabar EU Ursula von der Leyen.

Koriya ta Kudu, Mexico, Indiya, da sauran abokan cinikin Amurka da yawa sun ce za su daina aiki a yanzu yayin da suke neman rangwame kafin harajin da aka yi niyya ya fara aiki a ranar 9 ga Afrilu.

Jami’an Mexico sun ce za su ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Trump, yayin da

Canada ta ce tana bukatar yin garambawul ga tattalin arzikinta domin rage dogaro da Amurka, ta kuma sha alwashin mayar da martani kan harajin da Trump ya saka mata.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Da Kenya Sun Daukaka Dangantakarsu Yayin Da Xi Da Ruto Suka Gana

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Amurka Ta Fara Dandana Kudar Manufar Kakaba Harajin Kwastam
  • Sin Ta Musanta Yin Shawarwari Ko Tattaunawa Da Amurka Kan Batun Harajin Kwastam
  • Sin Da Kenya Sun Daukaka Dangantakarsu Yayin Da Xi Da Ruto Suka Gana
  • Tabbas Amurka Za Ta Cije A Yakin Haraji Da Ta Kaddamar A Duniya
  • Sin Ta Bukaci Amurka Ta Daina Siyasantar Da Batun Asalin Cutar COVID-19 
  • Hajjin 2025: Kashim Shettima Ya Jinjinawa Hukumar Alhazai Bisa Matakan Da Ta Dauka
  • Sin: Amurka Ta Buga Harajin Fito Kan Sassa Daban Daban Ba Tare Da Nuna Sanin Ya Kamata Ba
  • Kungiyar BRICK Ta Rattaba Hannu A Kan Yarjeniyar Raya Ayyukan Noma A Duniya
  • Illolin Da Manufar Haraji Kan Kayayyaki Ta Haifar A Kan Amerikawa
  • Yakin Ciniki Kalubale Ne Kuma Dama Ce Ga Nahiyar Afirka