Isra’ila ta sake kai hare-hare ta sama kan kasar Siriya
Published: 4th, April 2025 GMT
Jiragen yakin Isra’ila sun kai karin hare-hare ta sama kan kasar Siriya, inda suka bijirewa gargadin Majalisar Dinkin Duniya game da hadassa asarar fararen hula yayin da suke ci gaba da kai wa kasar ta Larabawa hare-hare.
Rahotanni sun ce a ranar alhamis, jiragen saman Isra’ila sun kai hare-hare a kalla sau biyu a kan wuraren da sojoji a kusa da birnin Damascus, inda bayanai suka ce sun kai hari a yankunan Al-Kiswah da Al-Muqaylibah.
Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka.
Hare-haren sun zo ne kasa da kwana guda bayan hare-haren da Isra’ila ta kai makamancin haka inda ta kashe mutane 13.
Fararen hula 9 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a lardin Dara’a da ke kudu maso yammacin kasar Siriya a yammacin ranar Laraba.
Isra’ila dai ta tsananta kai hare-hare kan Siriya tun bayan da ‘yan tawayen HTS suka karbe iko daga hannun gwamnatin Bashar Al’Assad a watan Disambar bara.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria Geir Pedersen a ranar Alhamis ya yi Allah wadai da karuwar hare-haren soji da gwamnatin Isra’ila ke yi, yana mai gargadin cewa suna yin zagon kasa ga yunkurin sake gina kasar Syria da kuma kara jefa kasar cikin mawuyacin hali.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce “Irin wadannan ayyuka na kawo cikas ga kokarin samar da sabuwar kasar Siriya mai zaman lafiya da yankin, da kuma jefa Siriya a cikin wani mawuyacin hali.”
Tun bayan rugujewar gwamnatin Bashar al-Assad, sojojin Isra’ila ke kai hare-hare ta sama a kan cibiyoyin da suke bayyanawa da na soji, da kuma rumbun adana kayan yaki na sojojin Siriya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kai hare hare kasar Siriya
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Gaza Suna Tsananin bukatar Agaji Da Kiran A Tilastawa Gwamnatin Mamayar Isra’ila Bude Mashigar Yankin
Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu
Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza, yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.”
Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa ta hanyar kai hare-hare wuce gona da iri kan wuraren dafa abinci da wuraren jin dadin jama’a, wadanda ke ba da taimako kadan ga matalauta da mabukata. Ya yi kira da a gaggauta bude mashigar kai daukin gaggawa zuwa Gaza, tare da ba da izinin gabatar da agajin jin kai, irin abinci, da magunguna cikin Gaza ba tare da wani bata lokaci ko sharadi ba, don ceton rayukan mutane da dama.