Aminiya:
2025-04-04@23:16:36 GMT

Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike

Published: 4th, April 2025 GMT

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ya yanke jiki ya faɗi har aka kai shi asibiti a ƙasar waje.

Ya ce wannan ƙarya ce da maƙiyansa na siyasa suka ƙirƙira don kawar da hankalin mutane.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu

Wike, ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyara wajen wani aiki da ake shirin ƙaddamarwa a watan gobe domin bikin cikar Shugaba Bola Tinubu shekara biyu a mulki.

A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Anthony Ogunleye, ya fitar, Wike ya ce waɗanda ke yaɗa wannan labari suna ƙoƙarin juyar da hankalin jama’a daga batun da tsohon shugaban ma’aikatan Jihar Ribas ya fallasa na yunƙurin saka bam a majalisar dokokin jihar da kuma hari kan kadarorin gwamnati.

“Babu inda na yanke jiki na faɗi, balle har a fitar da ni zuwa ƙasar waje.

“Ko a ranar da Shugaba Tinubu ya yi buɗa-baki kan zagayowar ranar haihuwarsa na halarta.

“Haka kuma, a ranar Sallah na jagoranci mazauna Abuja zuwa taya shi barkar da sallah. Ba zan damu da irin waɗannan jita-jitar siyasa ba, kuma ba za su hana ni aiki ba,” in ji Wike.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: karya Siyasa yanke jiki

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Ta Sanar Da Daukar Matakan Hana Fitar Da Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje Kan Wasu Ma’adinan Da Ba Kasafai Ake Samun Su Ba

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin tare da hadin gwiwar babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta sanar a yau Juma’a cewa, za ta fara aiwatar da matakan kiyaye fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje kan nau’o’in ma’adinai bakwai matsakaita da masu nauyi da ba kasafai ake samun su, wadanda suka hada da samarium, gadolinium, terbium, dysprosium, lutetium, scandium da yttrium. Kuma wannan sabon mataki ya fara aiki nan take.

Har ila yau, ma’aikatar ta sanar cewa, ta yanke shawarar kara wasu kamfanonin Amurka 16 da ke barazana ga tsaron kasa da moriyarta a cikin jerin sunayen kamfanonin da ta dauki matakin hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a kansu, tare da sanya kamfanonin Amurka 11 cikin jerin sunayen kamfanonin da ba su da tabbas, yayin da ta sanar da kaddamar da wani binciken yaki da shigo da kayayyaki fiye da kima kan shigo da wasu na’urorin daukar hoton CT na x-ray wadanda suka samo asali daga Amurka da Indiya.

Kazalika, babbar hukumar kwastam ta kasar Sin a yau Juma’a har ila yau, ta dakatar da takardun cancantar shigo da kayayyakin wasu kamfanoni shida na Amurka sakamakon batutuwan da suka shafi bincike da kuma kandagarkin kayayyakinsu. (Mohammed Yahaya)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai
  • Kasar Sin Ta Sanar Da Daukar Matakan Hana Fitar Da Kayayyaki Zuwa Kasashen Waje Kan Wasu Ma’adinan Da Ba Kasafai Ake Samun Su Ba
  • Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi
  • Yadda yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi
  • Nazari Kan Ayyukan Layin Dogo Biyar Da Za Su Ƙara Haɓaka Tattalin Arziƙin Nijeriya
  • Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP
  • APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027
  • Wike Ya Musanta Jita-jitar Faɗuwa Ta Rashin Lafiya
  • Aljeriya ta bukaci taron gaggawa a kwamitin tsaro kan Falasdinu