Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu
Published: 4th, April 2025 GMT
Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa.
Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa ya aike da takardar murabus ɗinsa kimanin makonni biyu da suka wuce, inda ya ce dalilansa na ƙashin kai ne.
Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance TaHar yanzu ba a tabbatar da ko fadar shugaban ƙasa ta amince da murabus ɗin ba.
An naɗa Baba-Ahmed a watan Satumban 2023 a matsayin mai bai wa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, shawara kan harkokin siyasa.
A lokacin da yake riƙe da muƙamin, ya wakilci gwamnati a taruka da dama na ƙasa da na siyasa.
Sai dai ya sha suka a shekarar 2024, bayan da ya samu saɓani da Ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro, Bello Matawalle, kan kalaman da suka shafi Ƙungiyar Tsofaffin Shugabannin Arewa (NEF), inda ya taɓa zama kakakinta kafin naɗinsa.
“Sukar NEF da Matawalle ya yi bai dace ba. Ya fi dacewa ya bayyana irin gudunmawar da ministocin Arewa da sauran jami’an gwamnati irina ke bayarwa wajen inganta tsaro da rage talauci a yankin,” in ji Baba-Ahmed
Matawalle ya mayar da martani da cewa: “Dukkanin wanda Shugaba Tinubu ya naɗa, ciki har da Dokta Baba-Ahmed, na da alhakin kare da kuma tallata ayyukan wannan gwamnati a fannoni daban-daban.”
Baba-Ahmed wanda ya taɓa zama Shugaban Ma’aikata na tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sananne ne wajen tsayawa kan gaskiya da adalci a harkokin ƙasa.
Kafin naɗin nasa, ya kasance Daraktan Yaɗa Labarai na ƙungiyar dattawan Arewa.
Tsohon babban jami’in gwamnati ne daga Jihar Kaduna kuma sananne ne a matsayin dattijo mai kishin Arewa.
Murabus ɗinsa ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a tsakanin masu bibiyar al’amuran siyasa a Arewa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gwamnatin tinubu Murabus Siyasa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi
SShugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana alhininsa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma’a yana mau shekaru 68 a duniya.
Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan Harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar, inda ya jaddada muhimmancin gudummawar Dr. Abdulaziz wajen koyar da addinin Musulunci da kuma ci gaban matasa.
Shugaba Tinubu ya yabawa ƙoƙarin marigayin wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da rikicin Boko Haram tun farkon bayyanar kungiyar. Ya ce al’ummar Musulmi sun yi babban rashi bisa mutuwar Dr. Abdulaziz wanda kan jajirce kan gaskiya da ɗa’a.
Shugaban ya kuma yi addu’a ga Allah Ya jikansa, tare da karfafa guiwar iyalansa da mabiyansa domin yin hakuri bisa wannan babban rashi da aka yi.
Daga Bello Wakili