Aminiya:
2025-04-04@23:09:38 GMT

APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027

Published: 4th, April 2025 GMT

Jam’iyyar APC, ta musanta jita-jitar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na shirin sauya Mataimakinsa, Kashim Shettima, kafin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce babu wata matsala tsakaninsu kuma maganar sauya Shettima ba ta da tushe.

Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu

Daraktan Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Bala Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ne ke yaɗa wannan jita-jitar don tayar da ƙura.

“Wannan jita-jita ce kawai marar tushe. Maganganu ne da bai kamata a ɗauke su da muhimmanci ba,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Ko da a ce akwai wani dalili da zai sa shugaban ƙasa ya sauya mataimakinsa, ba zai iya yin hakan shi kaɗai ba. Dole sai da shawarwari tare da masu ruwa da tsaki.”

Ko da yake APC ba ta bayyana aniyar Tinubu na sake yin takara a karo na biyu ba, magoya bayansa da wasu shugabannin jam’iyya sun fara neman goyon baya don ya sake tsayawa takara a 2027.

Wasu na ganin ya cancanci ya nemi wa’adi na biyu domin kammala ayyukan da ya fara.

A halin yanzu, wasu ’yan siyasa daga yankin Arewa ta Tsakiya suna kira da a ba su tikitin shugaban ƙasa ko mataimaki a zaɓe mai zuwa.

Sun ce tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1999, yankin bai taɓa samun shugaba ko mataimakin shugaban ƙasa ba.

Farfesa Nghargbu K’tso, wanda ya wakilci tawagar, ya ce: “Daga cikin yankuna shida na ƙasar nan, Arewa ta Tsakiya da Kudu Maso Gabas ne kaɗai ba su taɓa samar da shugaban ƙasa ko mataimaki ba cikin shekaru 26 da suka gabata. Lokaci ya yi da za a yi adalci da haɗin kai.”

Sai dai Bala Ibrahim, ya mayar da martani cewa buƙatar Arewa ta Tsakiya ba ta da tushe kuma “ta mutu tun kafin ta fara.”

Ya ce yankin bai taka gagarumar rawa a zaɓen da ya gabata ba bare ya nemi irin wannan buƙata, kuma ba yanzu ne lokacin tattauna rabon muƙamai ba, tunda Tinubu bai kammala wa’adinsa na farko ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sauya Mataimaki Zaɓen 2027

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi

SShugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana  alhininsa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma’a yana mau shekaru 68 a duniya.

 

Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan Harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar, inda ya jaddada muhimmancin gudummawar Dr. Abdulaziz wajen koyar da addinin Musulunci da kuma ci gaban matasa.

 

Shugaba Tinubu ya yabawa ƙoƙarin marigayin wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da rikicin Boko Haram tun farkon bayyanar kungiyar. Ya ce al’ummar Musulmi sun yi babban rashi bisa mutuwar Dr. Abdulaziz wanda kan jajirce kan gaskiya da ɗa’a.

 

Shugaban ya kuma yi addu’a ga Allah Ya jikansa, tare da karfafa guiwar iyalansa da mabiyansa domin yin hakuri bisa wannan babban rashi da aka yi.

 

Daga Bello Wakili

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi
  • Tinubu Zai Yi Amfani Da Dokar Ta-ɓaci Wajen Tsoratar Da Gwamnoni Gabanin Zaben 2027 – Amaechi
  • Shugaban Kasar Iran Ya Fadawa Muhammad Bin Salman Kan Cewa Tehran Tana Shirin Kare Kanta
  • Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu
  • Wike Ya Musanta Jita-jitar Faɗuwa Ta Rashin Lafiya
  • Rundunar PLA Ta Kaddamar Da Atisaye A Yankunan Tsakiya Da Kudancin Zirin Taiwan 
  • Tinubu Ya Tafi Faransa Ziyarar Aiki Na Mako 2
  • Shugaban Tinubu Ya Tube Kyara A Matsayin Shugaban Kamfanin NNPC Ya Kuma Sannan Ya Maye Gurbinsa
  • Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC