Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP
Published: 4th, April 2025 GMT
Kotun Ƙoli ta soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta yanke wanda ya amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP na ƙasa.
A ranar Juma’a, wani kwamitin alƙalai biyar na Kotun Ƙoli, ya ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta da hurumin yanke hukunci kan shugabancin jam’iyyar.
APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027 NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance TaAlƙalai sun bayyana cewa batun shugabanci al’amari ne da ya shafi cikin jam’iyya, kuma ba kotu ke da ikon yanke hukunci a kai ba.
Kotun ta kuma ce wa’adin mulkin Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar ya ƙare tun da farko.
Kotun ta amince da ƙarar da Sanata Ester Nenadi Usman da wani mutum suka shigar.
Sai dai ta yi watsi da ƙarar da ɓangaren Abure ya shigar, inda ta bayyana cewa ba ta da amfani.
Wannan hukunci na shugabancin Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP ya ƙare hukumance.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jam iyyar LP Kotun Ɗaukaka Kara
এছাড়াও পড়ুন:
Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Matashin Da Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kano
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp