Yadda yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi
Published: 4th, April 2025 GMT
Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz.
Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — WikeYa je ƙasashen Masar da Saudiyya domin neman magani kafin watan Ramadan.
Tun da safiyar ranar Juma’a, ɗaruruwan ɗalibansa da mabiyansa daga Bauchi, maƙwabtan garuruwa da kuma wasu jihohi sun taru a gidansa domin halartar jana’izarsa.
An gudanar da sallar jana’izar a ranar Juma’a a filin Idi na Games Village.
Manyan malamai, ’yan siyasa, ’yan uwa da abokan arziƙi da kuma mazauna birnin Bauchi sun halarci jana’izar.
Aminiya ta ruwaito cewar lokaci na ƙarshe da aka gan shi a bainar jama’a shi ne a ranar Sallah, inda ya yi wa al’ummar Musulmi jawabi bayan sallar Idi, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da juna.
Ga hotunan yadda jana’izar ta gudana:
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rashin lafiya rasuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta miƙa Janar Tsiga da wasu ga NSA
Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.
Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare da wani tsohon Ambasada da sauran waɗanda ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
Gobara ta lalata wani ɓangare na gidan Ado Bayero Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a TarabaAminiya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da tsohon shugaban Hukumar NYSC daga mahaifarsa a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 2025.
Da yake jawabi gabanin miƙa su a hukumance, Shugaban Cibiyar NCTC, Manjo-Janar Adamu Laka, ya bayyana cewa jami’an tsaro daga sojoji, jami’an DSS, ’yan sanda da sauran hukumomin sun yi aiki ba dare ba rana domin ganin an ceto su.