Aminiya:
2025-04-25@06:02:34 GMT

Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi

Published: 4th, April 2025 GMT

Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz.

Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike

Ya je ƙasashen Masar da Saudiyya domin neman magani kafin watan Ramadan.

Tun da safiyar ranar Juma’a, ɗaruruwan ɗalibansa da mabiyansa daga Bauchi, maƙwabtan garuruwa da kuma wasu jihohi sun taru a gidansa domin halartar jana’izarsa.

An gudanar da sallar jana’izar a ranar Juma’a a filin Idi na Games Village.

Manyan malamai, ’yan siyasa, ’yan uwa da abokan arziƙi da kuma mazauna birnin Bauchi sun halarci jana’izar.

Aminiya ta ruwaito cewar lokaci na ƙarshe da aka gan shi a bainar jama’a shi ne a ranar Sallah, inda ya yi wa al’ummar Musulmi jawabi bayan sallar Idi, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da juna.

Ga hotunan yadda jana’izar ta gudana:

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Rashin lafiya rasuwa

এছাড়াও পড়ুন:

2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasa Na Gwamnan Bauchi Sun Bayyana

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira A Ranar Juma’a A Maiduguri
  • Gwamnatin Haramtacciyar Isra’ila Tana Azabtar Da Falasdinawa A Gidajen Kurkukunta
  • Sabbin Haraji: Yadda ‘Yan Bindiga Ke Tilasta Wa Jama’a Biyan Miliyoyin Kuɗi A Zamfara
  • Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan mutuwar Fafaroma Francis
  • Za’a Yi Zana’izar Paparoma Francis A Ranar Asabar 26 Ga Watan Afrilu
  • Iyalen Surajo Malumfashi na Radio Nigeria Kaduna Yana Gayyatar Jama’a Zuwa Daurin Auren ‘Yar Sa
  • Yakin Ciniki Kalubale Ne Kuma Dama Ce Ga Nahiyar Afirka
  • Za A Yi Jana’izar Fafaroma Francis A Ranar Asabar A Vatican
  • Iran Ba Ta Da Niyyar Tattaunawa Da Amurka A Fili Bainar Jama’a Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya
  • 2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasa Na Gwamnan Bauchi Sun Bayyana