Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya.

“Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki.

“Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a duba abun da za a yi na gaba kan wannan batun hada-hadar mai da kudin naira,” cewar majiyar wanda ya nemi a dakaye sunansa.

Idan za a tuna dai, a ranar 1 ga watan Oktoban 2024 ne gwamnati ta fara sayar da danyen mai a kan naira ga matatar man dangote domin inganta samar da man fetur, lamarin ya kai ga taimaka wa kasar nan da samun rarar miliyoyi na dala da take narkawa wajen sayo danyen mai daga kasashen waje, kuma shirin ya taimaka sosai wajen samun ragi kan farashin fetur.

A baya-bayan nan, kakakin kamfanin NNPC, Olufemi Shoneye yayin da ke fashin karin haske kan batun karewar hada-hadar cinikin, inda ya ce, “Bari na fayyace wannan lamarin, daman an kulla yarjejeniya ce na watanni shida, ya danganci wadatar danyen mai, kuma zai kare ne a karshen watan Maris na 2025.

“Tattaunawa na ci gaba da gudanar kan yadda za a kulla sabuwar yarjejeniya.

“A karkashin wannan yarjejeniyar, NNPC ya samar da danyen mai sama da ganga miliyan 48 ga matatar dangote tun watan Oktoban 2024.

“A takaice, NNPC ya samar da danyen mai ganga miliyan 84 ga matatar tun lokacin da ta fara aiki a shekarar 2023.

“NNPC ya himma wajen samar da danyen mai ga matatun mai na cikin gida a bisa tsarin yarjejeniya da sharuddan da aka cimma,” ya shaida.

Kazalika, rahoton S&P ya nuna cewa matatar mai ta dangote ta sayo danyen mai na farko ne daga kasar Burazil da Ekuatorial Guinea.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Naira

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sauke Mele Kyari daga shugabancin Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL).

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar da safiyar Laraba ta tabbatar da naɗa Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ana Zargin Wani Ɗansanda Da Kisan Wata Mata Kan Cin Hancin Naira 2,000 — Bincike
  • Masarautar Hadejia Ta Raba Zakka Ta Fiye Da Naira Biliyan 1 Ga Mabuƙata 
  • Hakeem Baba-Ahmed ya yi murabus daga gwamnatin Tinubu
  • Madatsar Tiga Za Ta Samar Da Ruwan Sha A Garin Rano
  • IMF ta nemi Tinubu ya kyautata rayuwar talakawan Najeriya 
  • Babban daraktan hukumar IAEA, Rafael Grossi, zai ziyarci Iran cikin makwanni masu zuwa
  • Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m
  • Yadda Sabon Tsarin Harajin Kwastam Na Amurka Ke Shirin Gurgunta Tsarin Kasuwanci Na Duniya
  • Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC