Kasar Sin Na Nuna Damuwa Sosai Kan Harin Intanet Da Aka Kai Mata
Published: 4th, April 2025 GMT
A jiya Alhamis 3 ga wata ne, cibiyar daukar matakan gaggawa kan matsalolin kwayar cutar na’ura mai kwakwalwa ta kasar Sin, gami da ofishin gwajin ayyukan fasahohin magance kwayar cutar na’ura mai kwakwalwa na kasar, suka bullo da wani rahoto, kan binciken hare-haren yanar gizo da wasu kasashen waje suka kai kan tsarin adana bayanan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya karo na 9 da aka yi a birnin Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin a shekara ta 2025, gami da wasu muhimman ababen sadarwa dake lardin na Heilongjiang, inda ya shaida yadda kasar Amurka ta kaddamar da hare-haren intanet, kan tsarin adana bayanan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 da aka yi a birnin Harbin, gami da wasu muhimman ababen sadarwa na lardin Heilongjiang, kana ana kyautata zaton cewa hare-haren sun samu goyon-baya daga gwamnatin Amurka.
Har wa yau, yayin ziyararsa yankin Caribbean kwanan nan, sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Antonio Rubio ya ce wai hanyar mota da kasar Sin ta shimfida a kasar Guyana ba ta da inganci sam, inda Amurka ta yi fatan samar mata da zabi na daban. Game da wannan batu, Guo Jiakun ya ce, ba kamfanin kasar Sin ne ya shimfida waccan hanyar mota ba, kuma tuni Guyana ta karyata labarin. Kasar Sin na ganin cewa, maimakon shafa wa kasar Sin bakin fenti, da rura wutar rikici, gara Amurka ta aikata wa sauran kasashe alheri na zahiri. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Gyara Kuskurenta Na “Kakaba Haraji Ramuwar Gayya”
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna.
Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar Sin da sauran kasashe, wanda hakan ya sabawa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya da matukar yin illa ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kana ya nanata cewa, babu wanda zai yi nasara a takaddamar cinikayya ko harajin fito, kuma kariyar cinikayya ba za ta samar da mafita ba.
A wani ci gaban kuma, kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin He Yadong ya bayyana a taron manema labaru na yau Alhamis cewa, kasar Sin a shirye take ta warware damuwar da ke tsakaninta da Amurka ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito da tuntubar juna. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp