Aminiya:
2025-04-04@23:07:47 GMT

An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu a Kudu

Published: 4th, April 2025 GMT

An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP).

Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba.

Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno

A yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safarar su zuwa jihohin Kudu maso Gabas.

Ta ce, sun gano su kuma sun ceto su a garin Aba, a Onitsha da kuma wani ɓangare na Jihar Imo tare da iƙirarin waɗanda suka yi safarar su da cewa su marayu ne.

Ta bayyana cewa, an damƙe masu aikata safarar ne a garin Gembu da ke ƙaramar hukumar Sardauna, a lokacin da suke gudanar da haramtattun aikinsu, wanda ya kai ga ceto yaran takwas, yayin da wasu da dama da aka yi safarar su ba a kai ga ceto su ba.

Waɗanda aka yi safarar ta su a ƙarshe sun sake haɗuwa da iyayensu a watan Maris 2025, sun tabbatar da cewa an sayar da su ba tare da sanin iyayen su ba.

“Bayan ɗaukar matakin gaggawa da ma’aikatar ta yi da kuma Hukumar NAPTIP, an dawo da takwas daga cikin yaran Jihar Taraba cikin lafiya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hukumar Hana Safarar Mutane ta ƙasa NAPTIP Taraba da aka yi safarar a Jihar Taraba yi safarar su

এছাড়াও পড়ুন:

Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato

Sama da gidaje 70 ne suka lalace da rumfuma a wata guguwa da ta yi ɓarna a unguwar Mabudi, Sabon Gida, da sauran unguwanni a ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mamakon ruwan sama da aka yi a daren Laraba, wanda ya biyo bayan ruwan sama, ya yi ɓarna matuƙa.

INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang

Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa kimanin gidaje 70 ne rufinsu ya ɗaga, yayin da wasu gine-gine suka ruguje.

Nanbol Nanzing, wani mazaunin ɗaya daga cikin unguwar da lamarin ya shafa, ya koka da yadda lamarin ya faru tare da yin kira ga gwamnatin jihar ta tallafa.

Shugaban ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu, Hon. Nanfa Nbin ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mista Iliya Bako.

A cewar sanarwar, kwamitin bayar da agajin gaggawa na Ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu, wanda shugaban Ƙaramar hukumar ya kafa, ya ziyarci gidajen da lamarin ya shafa domin jajantawa waɗanda lamarin ya shafa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan ma’aikatan ceto : MDD ta gargadi Isra’ila game da aikata laifin yaki
  • An Nada Shugaban Hukumar Fasahar Sadarwa Da Inganta Tattalin Arziki Ta Jihar Jigawa
  • Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba
  • Gwamnatin Jigawa Ta Yi Sabbin Nade-nade A Fannin Ilimi
  • Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato
  • Mamakon Ruwan Sama: Matafiya sun Maƙale a Taraba Sakamakon Ɓallewar Gada
  • Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa
  • ‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga, Sun Ceto Ɗalibai 2 A Nasarawa
  • DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta