De Bruyne Zai Bar Manchester City A Ƙarshen Kakar Wasanni
Published: 4th, April 2025 GMT
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, ya ce: “Ko muna so ko ba mu so, lokaci ya yi da za mu yi bankwana.”
Ƙungiyar Manchester City ta ce za ta shirya wani bikin bankwana na musamman domin girmama ɗan wasan kafin kakar ta ƙare.
De Bruyne ya koma City daga Wolfsburg a kan fan miliyan 55, kuma ya taimaka sosai wajen nasarorin da ƙungiyar ta samu, ciki har da lashe kofin Zakarun Turai karo na farko a tarihinta, inda suka doke Inter Milan a wasan ƙarshe a birnin Istanbul.
Sai dai ɗan wasan ya sha fama da rauni a ‘yan shekarun nan, inda ya shafe watanni biyar yana jinya a kakar da ta wuce.
A kakar bana, ya buga wasanni 26 kacal a dukkanin gasa.
De Bruyne, ya fara wasan ƙwallon kafa a kulob din Genk na Belgium, kafin Chelsea ta saye shi a watan Janairu 2012 a kan fan miliyan bakwai.
Ya buga wa Chelsea wasanni tara kacal sannan aka tura shi aro zuwa Werder Bremen, daga nan ya koma Wolfsburg a 2013, kafin komawarsa City.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Barin Kungiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp