Sayyid Husi: Hare-haren Amurka Ba Za Su Yi Tasiri Akan Karfinmu Ba
Published: 4th, April 2025 GMT
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi ya bayyana cewa; Al’ummar musulmi suna fuskantar manyan hatsari guda biyu, da su ka hada laifukan da HKI take tafkawa a Gaza, da kuma kokarin shafe hakkokin falasdinawa baki daya.
Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya kuma tabo batun keta tsagaita wutar yaki da HKI take yi a kasar Lebanon yana mai kara da cewa, keta hurumin kasar Lebanon da ‘yan sahayoniyar suke yi, ya isa har birnin Beirut.
Akan kasar Syria ma, jagoran na kungiyar Ansarullah na Yemen ya yi ishara da hare-haren da ‘yan sahayoniya su ka kai a cikin biranen Damascus, Hums da Dar’a.
Sayyid Abdulmalik al-Husi ya ce,abokan gaba sun mayar da keta hurumin kasashen al’umma abinda za su rika yi kodayaushe. Haka nan kuma ya ce ko kadan bai kamata a mayar da kisan da ake yi wa Falasdinawa ya zama wani abu da ake gani yana faruwa a kowace rana ba.
Sayyid Abdulmalik ya yi kira da a sake dawo da fafutukar da ake yi a duniya baki daya, ta nuna kin amincewa da abinda yake faruwa a Gaza ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Cilla Makamai Masu Linzami Kan Kataparen Jirgin Ruwan Yaki Mai Daukar Jirage Na kasar Amurka
Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin cruise a hare-haren da suka kai kan kataparen jirgin yaki mai daukarjiragen saman yaki na kasar Amurka da suke cikin tekun maliya a karo na ukku a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar ta Yemen na fada a jiya Talata, kan cewa sun yi amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a wadan nan hare-hare kan USS Harry S.Truman kuma saun sami bararsu kamar yadda aka tsara.
Labarun ya kara da cewa yakin yana ci gaba tsakanin bangarorin biyu. Kuma wadan nan hare hare sun zo ne saboda maida martanin hare-haren da jiragen yakin Amurka suke ci gaba da kaiwa a kan kasar ta Yemen.
Majiyar ta kara da cewa hare-hare da makamai masi linzami kan HKI ma zai ci gaba kamar yadda gwamnatin kasar ta tsara.
Gwamnatin Amurka dai ta shiga yaki da sojojin Yemen ne saboda kare HKI a kan kissan kiyashin da takewa mutanen Gaza, sannan da kuma hana shigowar abinci da bukatun mutanen yankin tun fiye da wata guda da ya gabata. Har’ila yau sojojin Yemen sun hana jiragen ruwa kasuwanci na HKI ko wadanda suke zuwa can wucewa ta tekun.