Saboda Rikicin Kasar Sudan Ta Kudu Shugaba Musaveni Ya Isa Birnin Juba
Published: 4th, April 2025 GMT
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya isa birnin Juba na kasar Sudan ta kudu a yau Juma’a, a kokarin lalubo hanyar warware dambaruwar siyasar da kasar take ciki da hana barkewar sabon yakin basasa.
Jim kadan bayan yi wa mataimakin shugaban kasar Riek Machar daurin talala a gidansa ne kasar ta shiga zaman dar-dar da fargabar sake komawa cikin yakin basasa.
Da akwai kawance a tsakanin shugabannin kasashen Uganda Mosaveni da kuma Silva Kiir na kasar Sudan Ta Kudu. Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai kasar ta Uganda ta aike da sojoji masu yawa zuwa kasar ta Sudan ta Kudu, domin bayar da kariya ga gwamnatin Juba.
Gwamnatin Salva Kir tana zargin Machar da cewa yana rura wutar wani sabon yaki a cikin kasar. A ranar Laraba ta makon da ya shude ne dai aka yi wa mataimakin shugaban kasar daurin talala a gidansa saboda fadan da ake yi a yankin Upper Nile tsakanin sojojin gwamnati da kuma masu dauke da makamai na rundunar “White Army”.
Tawagar tarayyar Afirkan da ta isa birnin Juba wacce ta kunshi majalisar dattijan nahiyar Afirka, a kokarin shawo kan rikicin da kasar ta fada.
Tarayyar Afirkan ta fara kokarin shiga tsakani ne, bayan daurin talala da aka yi wa mataimakin shugaban kasa Riek Machar a gidansa,lamarin da ya sake jefa kasar cikin zaman dar-dar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp