Manyan Cibiyoyin Kudi Na Duniya Sun Yi Gargadai Akan Sabbin Kudaden Fito Na Amurka
Published: 4th, April 2025 GMT
Kungiyar kasuwanci ta duniya ( WTO) da asusun bayar da lamuni ( IMF) sun yi gargadi akan sakamakon dake tattare da Karin kudaden fito na kasuwanci da gwamnatin shugaban kasar Amurka Donald Trump ta yi a jiya Alhamis.
Kungiyar kasuwancin ta duniya, ta yi hasashen cewa ci gaban harkokin kasuwanci a duniya zai sami koma baya da kaso 1% a cikin 2025, wanda hakan yake nufin akasin yadda aka yi hasashe tun da fari.
Babbar daraktar kungiyar kasuwancin ta duniya Ngoz Okonjo-Iweala ta yi gargadin cewa, Karin kudaden fito da aka yi zai iya jefa duniya cikin yakin kasuwanci, idan kuwa kasashe su ka dauki matakin mayar da martani, to za a sami tsaiko a cikin harkokin kasuwanci a duniya.
Shi kuwa asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ta bakin shugabarsa Kristalina Ivanova Georgieva, ya bayyana cewa; Wadannan matakan da aka dauka za jawo hatsari mai girma wajen ci gaban da tattalin arzikin duniya yake yi, musamman ma a wannan lokacin da dama ake fama da tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin na duniya yake yi.
A gobe Asabar ne dai sabon harajin na Amurka zai fara aiki, wanda ya fara daga Karin 10% akan kayan da ake shigar da su Amurka, zuwa fiye da haka gwargwadon yadda ake da gibi a tsakanin kowace kasa da Amurkan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Daba Wa Kanta Wuka Bisa Karin Harajin Da Ta Yi
Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare da sauran abokan hulda. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp