HausaTv:
2025-04-26@02:42:34 GMT

Al-Azhar ta yi kira da a kama Netanyahu a matsayin mai laifin yaki

Published: 5th, April 2025 GMT

Cibiyar da ke sa ido kan tsattsauran ra’ayi da ke karkashin cibiyar ilimi ta Al-Azhar ta Masar, ta fitar da wata sanarwa da ta yi kira da a kame firaministan Haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a matsayin mai laifin yaki.

Shafin sawtbeirut.com ya bayar da rahoto kan sanarwar da ke cewa, cibiyar yaki da tsattsauran ra’ayi ta Al-Azhar, ta yi Allah wadai da tarbar da kasar Hungary ta yi wa firaministan Isra’ila, wanda ke fuskantar sammaci na kasa da kasa da kotun ICC ta bayar, ta kuma sanar da cewa: “Manufar wannan mataki shi ne tauye matsayin kotun kasa da kasa da kuma keta hurumin ta.

Sanarwar ta ce: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa alama ce ta tabbatar da adalci a duniya, kuma dole ne kasashen duniya su hada kai wajen mara mata baya wajen hukunta masu aikata laifukan yaki.

Kungiyar ta bayyana cewa: shawarwarin kasa da kasa da hukunta wadanda suka aikata laifukan yaki shi ne ginshikin tabbatar da zaman lafiya da adalci, kuma mutane suna da daidaito a gaban doka, babu wani wanda yake a birbishinta.

Sanarwar ta ce: “Babu lokacin yin shiru kana bin da yake fruwa, domin yin shiru yana halasta sabbin laifuka, kuma Gaza ta kasance share fage ne kawai ga ci gaba da aiwatar da bakaken manufofi da zubar da jini, da kashe rayuka.

An fitar da wannan sanarwa ne bayan da kasar Hungary ta yi maraba da firaministan Isra’ila duk da cewa kotun kasa da kasa  ta bayar da sammacin kama shi.

A watan Nuwamba 2024, Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ba da sammacin kama Benjamin Netanyahu bisa zargin aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama a Gaza.

Duk da wannan hukuncin, Netanyahu ya isa kasar Hungary inda ya gana da firaministan kasar Viktor Orban.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sharhin Bayan Labarai: Shin Kissan Mutanen Gaza Gaba Daya

Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan ‘wani makircin da kasar faransa ta kullawa falasdinawa a gaza’ don su amfana da kwararrunsu’ wanda ni tahir amin zan karanta.

///… Shugaba kungiyar kare hakkin bil’adama masi suna [the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor] ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da HKI na fitar da kwararru da kuma masana falasdinawa da suka rage a Gaza, zuwa wajen yankin, kafin HKI ta fa wani gagarumin kissan kiyashi a yankin kashe falasdinawa da suka rage a yankin.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Ramy Abdu shugaban kungiyar na fadar haka, ta kuma kara da cewa, offishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Qudus da aka mamaye, yana aiki tare da HKI don zakulo masana da kwararru a fannonin ilmi daban daban da ke tsare a cikin zirin gaza, zuwa wajen yankin saboda amfani da su don amfanin kansu.

Rahoton ya kara da cewa, wadanda zasu fitar daga yankin na Gaza, sun hada da dukkan masu digiri na uku wato PHD, likitoci, inginiyoyi, masanan tarihi da kuma wadanda suke da korewa a abubuwan al-adu da kayakin tarihi .

Kamfanin dillancin labaran Parstoday a kara da cewa wannan shi ne  wannan gagarumin aiki mikirce ne tsakanin Faransa da sojojin HKI na korar Falasdinawa daga Zirin gaza. Wannan shirin, inji Ramy Abdu ya sabawa dokokin kasa da kasa, kuma kasar faransa ta fada cikin wannan laifin wanda ake iya gurfanar da kasar da ta aikata haka a gaban kuliya.

Abdu ta kara da cewa abinda HKI ta kasa samu tare da amfani da makami tana son ta yi amfani da kungiyoyin kare hakkin bil’adama don cimma wanna manufar.

Kafar yada labarai da kasar Burtaniya mai suna ‘Middle East Eye’ HKI ta fara wani shiri na musamman, mai matakai 5 don tabbatar da ba wani bafalasdine da ya rage a Gaza, wanda kuma zai bata damar kafa kasar “yahudawa zalla’ a kan kasar Falasdinu.

Yahudawan sun sha nanata manufarsu ta ganin dukkan falasdinawa sun fice daga Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan tun bayan an fara yakin 7 ga watan Octpba shekara ta 2023.

Jaridar ta kara da cewa gwamnatin HKI ta fara aiwatar da wannan shirin, yana da matakai 5, kuma sun hada da, saka Falasdinawan cikin yunwa, rage yawan falasdinawa a gazar ta hanyar kashe su matukar iyawarsu, da lalata tsarin kiwon lafiya, ta yadda dan karamin cuta zata kashesu, maida gaza wurin da ba wanda zai ita rayuwa cikinsa,  sannan daga karshe anfani da dokokin kasa da kasa na maida gaza bangare na HKI bayan sun kammala kashe sauran falasdinawa a yankin.

Wannan ya nuna cewa zasu kashe falasdinawa kimani miliyon 2 a cikin karamin. Don haka a wannan tsarin suna ganin a mataki na 5 sun kammala kashe dukkan falasdinawa a gaza.

Jaridar ta kammala da cewa idan wannan shirin bai yi aiki ba suna da wani tsari wanda zai kasu ga shafe dukkan Falasdinawa a gaza. A cikin watan Jenerun wannan shekara ne shugaban kasar Amurka Donal trump ya bayyana wannan ra’ayin. Sai dai wannan ba ra’ayinsa na karan kansa ba, ra’ayi ne na yahudawan na samar da kasar yahudawa zalla tun asali.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muscat Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin Domin Ci Gaba Da Tattaunawa Da Amurka
  • Iran Ta Musanta Zargin Nethalands Na Cewa Tana Da Hannun A Kokarin Kisa A Kasar
  • Duniyarmu A Yau: Shiri Kasashen Yamma Na Kashe Dukkan Falasdinwa A Gaza
  • Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)
  • Sharhin Bayan Labarai: Shin Kissan Mutanen Gaza Gaba Daya
  • ICC ta ki amincewa da bukatar Isra’ila na soke sammacin kama Netanyahu
  • Mutum 7 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Fyaɗe Da Kashe Budurwa A Bauchi
  • Kasar Iran Ta Bayyana Cewa Kakaba Takunkumi Kan Kasarta Ya Sabawa Hikimar Gudanar Da Zaman Tattaunawa Da Ita
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana China Da Rasha A Matsayin Abokai Na Tushe Ga Iran
  • Al’ummar Gaza Suna Tsananin bukatar Agaji Da Kiran A Tilastawa Gwamnatin Mamayar Isra’ila Bude Mashigar Yankin