HausaTv:
2025-04-05@14:16:58 GMT

Pezeshkian: Iran ba ta neman yaki da kowace kasa

Published: 5th, April 2025 GMT

Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce Iran ba ta neman yaki da kowace kasa, amma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kanta saboda tana da kyakkyawan shiri a kan hakan.

Da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta shiga yin shawarwari don warware wasu matsaloli, bisa maslaha da mutunta juna, inda ya kara da cewa: “Ba ma neman yaki da wata kasa, amma ba mu da wani shakku wajen kare kanmu, kuma mun riga mun shirya tsaf dangane da hakan.

Shugaba Pezeshkian ya mika sakon taya murna ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya, da sarkin kasar, da kuma al’ummar kasar ta Saudiyya dangane da idin karamar Sallah.

Ya ce kasashen musulmi ta hanyar dogaro da kansu zasu iya  karfafa hadin kai a tsakaninsu, tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ci gaba a dukkanin matakai.

Shugaban ya kara da cewa, idan musulmi suka hada karfi da karfe, za su iya hana zalunci da laifukan da ake yi wa wasu kasashen musulmi da suka hada da Falasdinu da al’ummar Gaza, shugaban ya kara da cewa: Ina da tabbaci a kan cewa kasashen musulmi ta hanyar yin aiki tare za su iya samar da tsaro da wadata a yankin.

A nasa bangaren yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Bin Salman ya taya shugaba Pezeshkian da al’ummar Iran murnar idin karamar salla, inda ya bayyana jin dadinsa ga kiran da shugaban kasar Iran ya yi na hadin kai tsakanin al’ummar musulmi.

Ya kuma bayyana fatan cewa, karfafa hadin gwiwa tsakanin Iran da Saudiyya zai  samar da ci gaba mai ma’ana da kwanciyar hankali, tsaro, da ci gaba a yanking abas ta tsakiya.

Yarima mai jiran gado na Saudiyya ya kara jaddada cewa, hadin gwiwa tsakanin kasashen Iran, Saudiyya da sauran kasashe na iya inganta zaman lafiya a yankin, yana mai jaddada aniyar Riyadh na taimakawa wajen tinkarar duk wani kalubalen da ke da nasaba da kawar da ta’addanci a yankin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Rundunar PLA Ta Kasar Sin Ta Kammala Atisayen Hadin Gwiwa Na Kwanan Nan

 

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al-Azhar ta yi kira da a kama Netanyahu a matsayin mai laifin yaki
  • Yadda Musulman Nijeriya Suka Gabatar Da Bikin Ƙaramar Sallah Cikin Matsin Tattalin Arziƙi
  •  Limamin Tehran: Babbar Jarabawar Dake Gaban Al’ummar Musulmi Ita Ce Kare  Al’ummar Falasdinu
  • Shugaban Kasar Iran Ya Fadawa Muhammad Bin Salman Kan Cewa Tehran Tana Shirin Kare Kanta
  • Iran ta yi kira ga kungiyar Shanghai ta yi Allah wadai da barazanar Trump
  • Rasha ta gargadi Amurka kan duk wani gigin ka wa kasar Iran hari
  • Rundunar PLA Ta Kasar Sin Ta Kammala Atisayen Hadin Gwiwa Na Kwanan Nan
  • Araghchi : Iran a shirye take don tattaunawa amma barazanar soji daga Amurka na dagula yanayin’
  • Neman “’Yancin Kan Taiwan” Da Jam’iyyar DPP Ke Yi Zai Ci Tura