Ɗaliban Kano za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnati
Published: 5th, April 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025.
Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025.
Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labaraiGa ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata.
Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara sun koma makaranta a kan lokaci.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dokta Ali Haruna Makoda, ya gargadi ɗalibai da su guji kawo miyagun abubuwa kamar wuƙa, reza ko ƙwayoyi zuwa makaranta.
Ya kuma ce gwamnati za ta ɗauki mataki a kan duk ɗalibin da ya ƙi bin wannan doka.
Ya ƙara da cewa bin doka da ƙa’ida na taimaka wa ɗalibai su samu nasara a karatunsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗalibai gwamnati Komawa Makaranta Ma aikatar ilimi koma makaranta
এছাড়াও পড়ুন:
Kawu Sumaila ya koma APC
Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Sumaila ya tabbatar wa Aminiya ficewarsa a wani saƙon kar ta kwana, bayan wallafa wa a shafinsa na Facebook.
Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC“Gaskiya ne na koma APC. Damuwata a ko yaushe ita ce walwalar al’ummar mazaɓata,” in ji shi.
Sanatan ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka na sauya sheƙar ya yi shi ne domin inganta rayuwar al’ummar mazaɓarsa, da kuma tabbatar da ci gabansu mai dorewa.
Kawu dai ya daɗe da raba gari da tafiyar Kwankwasiyya da NNPP da ya yi takara ƙarƙashin ta, wanda ya sanya wasu da dama suka daɗe da hasashen zai sauya sheƙa zuwa tsohuwar jam’iyyarsa ta APC da ya bari a wancan lokacin.