Euro-Med : Laifukan da Isra’ila ta aikata a Gaza sun zarce na Daesh
Published: 5th, April 2025 GMT
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa Euro-Med ta ce Laifukan da Isra’ila ta aikata a Gaza sun zarce na kungiyar Daesh.
A rahoton data fitar Euro-Med ta ce, tawagoginta sun tattara dubban laifukan da sojojin Isra’ila suka aikata, wadanda suka zama shaidu masu yawa na cin zarafi.
“Wadannan laifuffukan suna wakiltar yanayin tashin hankalin da ba a taba gani ba a baya baya nan, saboda laifuka ne da akayi da gangan, da kuma manufar kisan kiyashi.
” Dole ne a yi tir da yanayin laifukan da Isra’ila ta aikata a cikin yankunan Falasdinawa, saboda girman wadannan laifuffukan, wanda ya zarce na kungiyar Daesh.
Har ila yau Euro-Med ta jaddada bukatar gaggawar daukar matakin da ya dace na kasa da kasa, da kawo karshen rashin hukunta Isra’ila da kuma matakin da ya dace na hana ci gaba da aikata ta’asar.
“An aikata wadannan laifuffukan ne tare da bayyanannun niyyar kawar da al’ummar Falasdinu, da murkushe wadanda suka saura a kasarsu, da shafe su, da kawo karshen wanzuwarsu baki daya.” Inji rahoton na Euro-med.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan kasar Labanon da Siriya yana da matukar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da ayyukan wuce gona da iri da na ta’addancin yahudawan sahayoniyya a Gaza da Lebanon.