Hukumar kula da shirye-shiryen fansho na wucin gadi, wato PTAD, ta nemi afuwar ’yan fansho a fadin Najeriya kan jinkirin biyan wasu daga cikin kudaden fansho da suka taru.

A wata tattaunawa ta waya da Shugaban Kungiyar Tsofaffin Ma’aikatan NIPOST na reshen Jihar Legas, Kwamared Mukaila Ogunbote, jami’an PTAD sun bayyana cewa jinkirin ya samo asali ne daga wasu matsaloli da suka shafi Babban Bankin Najeriya da kuma Ma’aikatar Kudi.

Sai dai hukumar ta tabbatar da cewa dukkan hakkokin da suka rage, ciki har da na wadanda aka sake rijista bayan tantancewar “Ina Raye”, za a biya su a cikin wannan watan.

Kwamared Ogunbote ya ce an tattauna batutuwa da dama da suka shafi walwalar ’yan fansho, kuma ya sha alwashin ci gaba da bibiyar lamarin har sai an warware matsalolin da ke tattare da shi.

Ya kuma roki hadin kai, fahimta da juriya daga tsofaffin ma’aikatan, domin a cimma mafita cikin ruwan sanyi, musamman ganin cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da sakin naira biliyan sittin da takwas domin biyan bashin.

 

Suleiman Kaura

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An Bude Kasuwar Baje Koli Na Man Fetur Da Gas Karo Na 29 A Nan Tehran

A yau ne aka bude kasuwar baje koli na kayakin da suka shafi man fetur da gasa wadanda aka kera a JMI karo na 29  a yau a nan birnin Tehran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kasuwar zata ci ne daga yau 8-11 ga wannan watan na mayu da muke ciki.

Labarinn ya kara da cewa kamfanoni fiye da 2000 daga ciki da kuma wasu kasashen duniya  14 ne suka halarta ta. Baje kolin yana nuna matsayin JMI a fagen makamashi a duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yi Aka Yi Bikin Haihuwar Tauraro Na 8 Daga Taurari 12 Wasiyyan Manzon Allah (s)
  • Jagora: Ma’aikata Su Ne Jari Mafi Girma Domin Cimma Manufar Bunkasa Tattalin Arziki
  • Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2
  • Bayan Cin Kamfanin META Tarar Dala Miliyan 220: Sun Yi Bazaranar Katse Kafofin Facebook, WhatsApp, Da Instagram A Nijeriya
  • Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare
  • Masana sun ƙalubalanci sojoji kan maharan ƙasashen waje
  • Masan sun ƙalubalanci sojoji kan maharan ƙasashen waje
  • NAJERIYA A YAU: Abin ya sa aka kasa kawo ƙarshen Tamowa a Arewa Maso Gabas
  • An Bude Kasuwar Baje Koli Na Man Fetur Da Gas Karo Na 29 A Nan Tehran
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Gamsu da Gudanar da Aikin Tantance ‘Yan Fansho