Leadership News Hausa:
2025-04-26@07:57:57 GMT

Wutar Lantarki: Badaƙala Da Cin Zalin ‘Yan Nijeriya

Published: 5th, April 2025 GMT

Wutar Lantarki: Badaƙala Da Cin Zalin ‘Yan Nijeriya

A Afrilun 2018, Hukumar Hadin Kan Kasa da Kasa ta Japan (JICA) ta ba da tallafin Yen na Japan biliyan 1.317 kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 12.4 (kimanin Naira biliyna 4.5) don shigar da na’urorin wutar lantarki (power capacitors da switchgears)

TCN a watan Satumbar 2019 ta ce ta samu lamuni na Dalar Amurka biliyan 1.

661 (kimanin Naira biliyan 601.3bn) daga hukumomi biyar don saye da sanya ayyuka a karkashin shirinta na ‘Rehabilitation and Edpansion Program’ (TREP).

Bankin Duniya shi ne ya fi bayar da gudunmawar inda ya bayara da Dalar Amurka miliyan 486 don sabon aikin isar da wutar lantarki ta Nijeriya mai taken (NETAP), da kuma Dalar Amurka miliyan 27 na aikin watsawa mai taken (North Core).

Bankin Raya Afirka (AfDB) ya ba da Dalar Amurka miliyan 410 don ayyukan fadada rarraba wutar lantarki, Hukumar Raya Kasashe ta Faransa (AFD) da Tarayyar Turai (EU) sun ba da Dalar Amurka miliyan 330 don aikin wutar lantarki mai taken (Northern Corridor Transmission Project).

A halin da ake ciki Nijeriya na da GENCOs 25, amma babban layukan wutar lantarki ta Nijeriya (National Power Grid) ta durkushe sau 206 daga shekarar 2010 zuwa 2019, kamar yadda Cibiyar Bincike ta Duniya (ICIR) ta ruwaito.  Kalubale ne samun alkaluma na  shekarun 2005 zuwa 2009 da kuma daga 2020 zuwa yau.

Duk da durkushewar layukan wutar lantarkin da ke faruwa, Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC), ta bayyana cewa za ta cire Naira biliyan 10.5 daga cikin ribar kudaden da aka amince kuma aka ba da izini  na shekara-shekara ga DISCOs guda 11, a matsayin wani vangare na takunkumi kan rashin bin ka’idojin lissafin kudi da za su caja  abokan cinikin su da ba su da mitoci.

Rahoton 2019 na Ofishin Kididdiga na Kasa (NBS) – Rahoton Sashen Makamashi da aka samu kuma aka tura (Energy Generated and Sent Out and Consumed and Load Allocation). Ya nuna:

Jimillar makamashin da GENCOs suka samar kuma aka aika, shi ne 33,448,633 MWh, kamar haka:

a.      GENCOs masu zaman kansu – 19,692,683 MWh. b.      Masu Samar da Wutar Lantarki (IPP) – 7,798,253 MWh. c.       Hadakar Wutar Lantarki ta Kasa (National Integrated Power Project (NIPP) – 5,957,697 MWh.

Ba ri muyi lissafi gwari-gwari: Matsakaicin Kirkirar Makamashi na Kullum =Jimlar Kirkirar Makamashi na Shekara-shekara / Yawan Kwanaki a cikin Shekara.

A.     Matsakaicin Karfafa Makamashi na Kullum = MWh 33,448,633 kwanaki 365. B.     Matsakaicin Karfafa Makamashi na Kullum = MWh /91,642.28  kowace rana.

A halin yanzu matsakaicin Rarraba Wutar Lantarki (MW) dangane da bayanan NERC kamar yadda ta sanar a shekarar 2021 ya kasance MW 4,094.09.

Tambaya a nan,

Na farko – Me ya faru da kiyasin makamashin MWh 87,000 (91,642.28 – 4,094.09) da ake samarwa a rana?

Na biyu – Me ya sa CBN da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi za su ci gaba da fitar da biliyoyin Naira don samar da makamashin da ba ya isa wajen masu bukatarsa?

Na uku – Menene kuma ya faru da makudan kudade na kasafin kudin shekara-shekara (National Budget) da suka shiga harkar wutar lantarki ba tare da samar da ingantacciyar wutar lantarki ga jama’a ba?

 

Cin Zali da Rana Tsaka

A lokacin da aka ruguza NEPA/PHCN, akwai ma’aikata kusan 15,000 da aka sallame su, sannan aka mayar da al’amuransu zuwa kamfanin kula da al’amura, da basususka da kuma sauran ababen da suka shafi  wutar lantarki  na Nijeriya, wato (NELMCO) wanda aka kirkira domin gudanar da ayyukan da ya shafe wa’anan ababe na rusasshiyar PHCN.

To wane wainar aka toya a wannan vangaren?

A cewar Bankin Lamuni (IMF), an kiyasta cewa Nijeriya ta na yin asarar kusan Dalar Amurka biliyan 29 a kowace shekara saboda rashin samar da wutar lantarki isasshe. Bugu da kari, an ruwaito ‘yan Nijeriya na kashe kudade  Dalar Amurka biliyan 14  kowace shekara akan janareta da mai don shawo kan karancin wutar lantarki.

Ba makawa rufe Kamfanin Mitar Wutar Lantarki na Nijeriya (EMCON) da take Zariya na Jihar Kaduna tare da asarar ayyukan yi da kuma fitar da makudan kudaden waje zuwa kasashen waje don sayen mitoci savanin sanya hannun jari a cikin gida.

NELMCO ce ke da alhakin rikewa da sarrafa kaddarorin PHCN da Yarjejeniyar Sayen Wutar Lantarki, tare da ikon siyarwa, ko mu’amala da wadannan kaddarorin don biyan basussuka ko wasu batutuwa masu alaka.

An dora wa NELMCO alhakin karva da gudanar da basussukan da suka makale, kuma ita aka daurawa alhakin sauran alamura da ke da alaka da albashi ko alawus na ma’aikatan rusasshiyar Kamfanin Power Holding Company of Nigeria (PHCN). wannan ya hada da:

Rashin biyan kudin Fansho da Garatuti na vangaren  gudummawar kamfanin NEPA/PHCN saboda kashi 7.5% kawai da ma’aikatan ke bayarwa ko wane wata su ne a cikin asusunsu na PFA.

Rashin biyan albashi da alawus-alawus da fakitin sallama na yawancin tsofaffin ma’aikatan kamfanin NEPA/PHCN.

Batu mai ban haushi da ya kunshi kaso 10% na hannun jarin kafanin PHCN na ma’aikatan da aka sallama wanda har yanzu ba a basu ba.

Wani batun kuma da aka kasa warware shi, shi ne horon salama (training) na gida da na waje da kuma bita ga ma’aikatan da aka sallama, wanda ya kasance sharadi ne na sallama ko biyan  alawus a madadinsa, har yanzu ba a biya su wannan kudade ba.

Rashin biyan asalin alawus da kuma bashin da suke bi na albashin watanni 16 daga 2012. (Daga lokacin ruguza kamfanin PHCN zuwa kammala mika su ga mutanen da wai su ne ’’Core Investors’’).

Rashin biyan  kuɗin inshoran  ma’aikatan NEPA/PHCN.

Rashin biyan kudin rangwamen wutar lantarki ga ma’aikatan NEPA/PHCN da aka sallama.

Halin da aka jefa wadanda aka sallama a lokacin wasoson NEPA/PHCN ya kara wani rashin adalci ga labarin, yayin da kuma aka bar su a cikin rudani, da kuma hana su hakkokinsu na hakika. Bayan haka, wadannan sallamammun ma’aikatan an bar su cikin wani yanayi na fargaba da rashin sanin makomarsu game da makudan kudadensu da ya haura kimanin Naira bilyyan 25 ko fiye, bisa ga ikirarinsu.

Bari mu nunfasa haka kada mu samu hawan jinni domin kuwa akwai saura.

Za mu ci gaba mako mai zuwa idan Allah ya kai mu.

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Lantarki Dalar Amurka miliyan wutar lantarki ta Wutar Lantarki ta da Wutar Lantarki da wutar lantarki Rashin biyan

এছাড়াও পড়ুন:

Manyan Bankuna 5 Da Suka Samu Ribar Naira Tiriliyan 17.3 A Nijeriya

Bankin Zenith ya kasance a kan gaba tare da samun ribar naira tiriliyan 1.32 kafin a biya haraji, wanda hakan ke nuna karin kashi 67 cikin 100 daga naira biliyan 796 da aka samu a shekarar 2023.

 

Bankin GTCO ya bi sahu, inda ya fitar da ribar kashi 107.8 kafin a fara biyan haraji zuwa naira tiriliyan 1.266, daga naira biliyan 609 na bara.

 

Har ila yau, Access Corp da UBA sun taka rawar gani sosai, inda suka samu ribar naira biliyan 867 da kuma naira biliyan 803.7, wanda ya zarce adadin da suka samu a shekarar 2023 na naira biliyan 729 da kuma naira biliyan 757.6.

 

First HoldCo ya kuma samu ribar kashi 124 cikin 100 na ribar da aka samu, daga naira biliyan 347.9 a shekarar 2023 zuwa naira biliyan 781.9 a shekarar da ta gabata.

 

Masu gudanarwa sun yi amanar cewa juriyar da fannin banki ke nunawa ba wai kawai shaida ce ga daidaitawar cibiyoyin hada-hadar kudi ba har ma da nunin damar da za a samu nan gaba, musamman ga masu saka hannun jari da ke sa ran samun kwanciyar hankali.

 

Ko da yake sun bayar da hujjar cewa, idan aka yi hasashen farashin kudin ruwa zai ragu, kuma nairar za ta kara karfi tare da rage sauyin yanayi, ribar bankunan na iya fuskantar matsin lamba a bana.

 

Duk da haka, kwararrun sun ci gaba da jajircewa kan fannin, tare da lura da cewa bankunan da ke da kakkarfan habakar lamuni da kuma dabarun samun kudin shiga maras riba, musamman wadanda ke yin amfani da ayyukan kasuwanci, da alama za su kasance masu jan hankali ga masu zuba jari.

 

Wani manazarci, Charles Abuede, ya ce ayyukan bankunan Nijeriya a cikin shekara ta 2024 suna ba da manuniya mai kyau ga abin da ke gaba a 2025.

 

Ya ce, akwai hasashen za a samu karin tagomashi sosai a bangarorin a shekarar bana, wanda a cewarsu ayyukan na kyau matuka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • A Karon Farko A Tarihi Adadin Lantarki Da Sin Ke Iya Samarwa Ta Karfin Iska Da Hasken Rana Ya Zarce Wanda Ake Iya Samarwa Ta Amfani Da Dumi
  • Manyan Bankuna 5 Da Suka Samu Ribar Naira Tiriliyan 17.3 A Nijeriya
  • Masana’antun Nijeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 1.11 Wajen Samun Wutar Lantarki A 2024 – Rahoto
  • Rashin Wutar Lantarki: Jihohin Kano, Katsina Da Jigawa Na Samun Wutar Awa 2 Ne Kacal A Kullum
  • Rage Farashin Man Fetur Na Dangote Ya Sa Wasu Gidajen Mai Na Kullewa
  • Sojonin Yemen Ta Kakkabo Jiragen Yakin Amurka Wadanda Kimarsu Ya Dalar Amurka Miliyon $200 A Makonni 6
  • **Gwamnati Za Ta Kwace Gidajen Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya Ba Su Biya Bashin Gidaje Ba
  • Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro
  • Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya
  • DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa