HausaTv:
2025-04-06@00:40:47 GMT

Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 103

Published: 5th, April 2025 GMT

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suak zo cikin al-kur’ani  mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na m,aulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).

A cikin shirimmu da ya gabata mun ji yadda Khalifa na biyu, a lokacinda ya zo mtuwa ya kafa shura na mutane 6 wadanda yace dukkaninsu manzon All…(s) ya yardadasu kafin ya bar duniya sannan ya bukaci su zabi daya daga cikinsu a matsayin khalifa a bayansa. Mun bayyana cewa ya sanya Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) daya daga cikinsu amma ya tabbatar da cewa ba zasu taba zabensa a matsayin Khalifa ba, saboda dalilain da ya kawo, na shugabantar da Abdurrahman dan Auf, wanda ya kasance surukin Uthman Dan Affan, sannan Sa’adu dan Abiwakkasa ba zai sabawa dan amminsa Abdurrahman dan Auf ba, Sannan dama Aliyu (a) baya shiri da Talha dan ubaidullah wanda ya nuna cewa a yawa Uthman zai fishi idan an raba biyu ma Abdurrahman dan Auf baya tare da shi.

Sannan munji yadda Khalifan ya aibatasu gaba daya, daga cikin har’da Amurul muminina (a) inda ya zargeshi da wargi da wasa, amma ya tabbatar da cewa idan da zasu bashi ita da ya kaisu kan hanya madaidaiciya, da kuma ya kaisu kan gaskiya.

Kafin haka yace da Salim maula Abu khuzaifa yana nan da ya nada shi Khalifa, sannan da Abu Ubaida dan jarrah yana nan da ya nadasu a matsayin Khalifa kai tsaye.

Idan muka koma baya zamu ga yadda wadannan mutane biyu suke tare da su a ranar wafatin manzon All…(s) da kuma rawan da suka taka wajen tabbatar da cewa Khalifanci ta fita daga hannun Amirul mumimina (s) ta kuma koma hannun Khalifa na farko.

Amma a cikin shirimmu na yau zamu ga yadda aka gudanar da Zaben khalifa a tsakanin mutane 6 wadanda Khalifa na biyu ya bada umurnin su zabi guda daga cikinsu.

Da farkon dangane da cancantar Amirul muminina da Khalifanci, Khalifa Umar bai fi manzon All..(s) sanin haka ba, don a aikace ya nada shi a Ghadir, sannan a lokacinda ya nada shi yace ‘wanda na kasance shugabansa to Aliyu wannan shugabansa ne” yace Ubangiji ka jibanci wanda ya jibance shi ka kuma tabar da wanda ya tabar da shi, ka kuma risker da gaskiya a gareshi a duk inda ya juya.  A wani hadisi, ya ce: Da zasu dora Aliyu da zasu sameshi shiryeyye mai shiryatarwa.

Malamai da dama sun bayyana ra’ayinsu dangane da shuraa ta Umar, kuma sun wadannan al-amura, daga ciki.

01-Ya shirya shura ne kawai don kauda Aliyu (a) daga Khalifanci, saboda ya sanya mafi rinjayen mambobin shoran makiyan Aliyu dan Abitalib (a) wadanda suka hada banu Umayya da Banu Taim. Wato dangin Khalifa na farko. Talha dan ammin Abubakar ne, banu taim, wanda yake adawa da Aliyu dan Abitalib (a). Saboda husuma da yayi da dan amminsa bayan wafatin manzon All..(s) dangane da Khalifanci. Da Uthman da Abdurrahman dan Auf, dangin Banu umayya ne wadanda suke ganin Aliyu ya kashe shuwagabannin su a manya-manyan yake-yaken da aka yi a farkon musulunci. Wato a yakin Badar da Uhudu, da Ahzab da.

Don a lokacinda Aliyu ya karmi khalifanci, Abdurrahman dan Auf ya na daga cikin wadanda suka ki yi masa bai’a bayanda mutane suka zabe shi, Aliyu bai tilasta masa ba.

2-Aliyu dan Abitaliba ya na daukar Zubair dan Awwam, a matsayin shi’arsa ne, saboda yana tare da shi a lokacinda aka kwace khalifanci daga wajensa bayan wafatin manzon All…(s). Zubair ya na gidansa sanda Umar da wasu sahabban suka shiga gidansa suka fitar da shi masallaci don yin bai’a.   

Don haka atakaice, Umar ya nufi ya kawar da Khalifanci daga Aliyu dan Abitalib (a) a wannan karon ma.

Sannan wani abin mamaka da shura, shi ne, Khalifa ya ce manzon All..(s) ya rasu yana mai yarda da wadan nan mutane 6, amma kuma yace idan sun wuce kwanaki uku basu zabi wani daga cikinsu ba, aka kashe su. Zababbun kuma wadanda manzon All…(s) ya yi wafati yana mai yarda da su ne za’a kashe? Abin mamaki.

Sannan yace: idan sun rabu gida biyu mutane uku uku, bangaren da Abdurrahman dan Auf yake ne zai zama mai rinjaye. Kamar babu Aliyu dan Abitalib (a) a cikinsu, ta yaya zai gwatanta Abdurraman dan Auf da Amirul muminina (a).? wanda Imam Ali (a) ya halaka danginsa kafirai da dama a yake-yaken badar da Uhud da sauransu.

Sai kuma taron zaben Khalifa, wanda wasu suka ce an yi shi ne Baitul Mali na lokacin a birnin Madina. Wasu kuma suka ce an yi shi a gidan wani mutum wanda ake kira. Musawwar dan Mukhrimah.

Sannan Imam Hassan (s) jikan manzon All..(s) ya halarci wannan taron na zaben khalifa, hakama Abdullahi dan Abbas ( r) , sannan Amru dan Asi da Mughirah dan shiab sun zo kusa da inda ake zabe,  a daya daga cikin wuraren nan biyu da muka ambata. Sannan yansanda jami’an tsaro na lokacin suka yiwa wurin kawanya, don tabbatar da cewa an aiwatar da wasiyyar Umar,

Don haka mutanen 6 suka zo kusa, sai Imam Aliyu dan Abitalib,(a) ne ya fara tashi, daga cikinsu ya yiwa mutanen nan 5 wa’azi ya gargade su, yace masu su ji tsoron All..su mayar masa da hakkinsa, wanda All..Ta’ala ya nada shi, manzon All..(s) ya kuma zartar da nadin, a wurare da dama a rayuwarsa.

Da ga karshen ya ja kunnensu kan cewa idan basu na da shi ba, to kuwa zasu ga abinda ba sa so a cikin al-ummar musulmi, zasu rarraba, sannan za’a sami wadanda zasu zubar da jinni musulmi don neman wannan kujerar ta Khalifanci ba tare da suna da hali guda mai kyau daya da ya bashi damar zama Khalifa ba.

Da ba’a zabeshi daga karshe ba, mun ga yadda Mu’awiya dan Abisufyan, wanda bai musulunta bas ai shekaru biyu kafin wafatin manzon All..(s) ya zo yana jayayya da Aliyu dan Abitalib (a), wanda shi ne farkon musulunta, sannan shine jarumin dukkan manya-manyan yake yake a musulunci, kamar Badar da Uhudu da Ahzab. Yana jayayya da shi kan khalifancin manzon All..(s). kuma sai da ya zama, tare da taimakon wasu manufurai, ba ma kawai shi ba, sai da yayansa da jikokinsa suka yi Mulki na shekaru fiye da 100 a bayansa a matsayin Khalifofin manzon All..(s).

Suka yiwa musulunci da musulmi barnan da ba’a taba gyaransa ba har duniya ta nade.

Sun yaki yayan manzon All..Tsarkaka sun koresu a bayan kasa, suka bisu a ko ina suka je a duniya suka kakkacesu. Don haka abinda Imam Ali(a) ya fada masu a taron zaben khalifa bayan mutuwar Umar duk sun faru.

A cikin littafin Tarikhin umammu wal-muluk ya kawo bangare na Khudubar Imam Ali a lokacin zaman zaben khalif ana ukku. Inda yake cewa:

{..ba wani wanda ya rika ni amsa kira zuwa gaskiya, da sada zumunci,..har zuwa inda yake cewa…ku saurari zance na, ku fahinci manufata, -idan baki yi abinda ya dace ba to kuma –da sannu zaku ga wannan al-amari (wato Khalifanci) ana zare takubba don nemansa, sannan a karya alkawulla da don nemansa, sai yak aiga wasu daga cikinsku sun zamo shuwagabannin bata, kuma magoya bayan mutanen jahiliyya} kamar yaddayazo cikin littafin sharhin Nahjul Balagh ana sheikh Muhammad Abduh..

Da masu shura sun ajiye son zuciyarsu gefe, sun dubi maslahar musulunci, suka mayarwa mai  hakki hakkinsa, da dukkan wadannan musibu basu sami al-ummar musulmi ba.

Don haka an yi ta ja yayya tsakanin wadanan mutane 6, a rana ta farko, sun kasa zaben day daga cikinsu, an sake yin taro a rana ta biyu an kasa zaben mutum daya. Kuma wasiyar Umar itace a kashe dukkan mutum shida idan sun kasa zaben daya daga cikinsu bayan kwanaki uku.

A nan sai Abu Talha Al-ansari, ya zo wajensu yana cewa, {Ba zan kara baku ko kwana guda ba, idan wa’adin kwanaki uku ya cika zamu zartar da wasiyyar Khalifa a kanku ne}.

A nan ne sai suka kulla wata zaman, sai Talha dan’ubaidullahi ya tashi yace ya bawa bawa Uthman kuri’arsa, wato ya zabi Uthman, wannan kuma a fili yake, saboda fitattun yan takarar sune Aliyu dan Abitalib (a) da kuma Uthman dan Affan. A nan sai Zubair ya tashi shi ma, sai yace, ya bawa Aliyu dan Abitalib (a) kuri’arsa.

Daga nan sai Sa’ad dan Abiwakkas ya tashi yace, ya bawa Abdurrahman dan Auf kuri’arsa, kada ku manta shi dan amminsa ne.

Sannan Abdurrahman ya ga cewa ba zai iya zama Khalifa a kan wadannan biyu ba, wato Aliyu ko Uthman, don haka sai ya nemi shawarar Kuraishawa, suka ce masa ya zabi Uthman.

A nan Abdurrahman bin Auf shi ne mai raba gardama, idan ya koma gefen Aliyu, (a) , shi ne Khalifa, don a lokacin zasu zama masu kuri’u 4. Aliyu, da Zubair da kuma Abdurrahman dan Auf da kuma Sa’ad dan Abiwakkas.

Idan kuma ya koma gefen Uthman, zasu zama ‘kuri’u 4 shi ma, ga Uthman da Talha, ga kuma Sa’adu da kuma shi Abdurrahman. A nan sai ya zabi komawa ga Uthman, sai Uthman ya zama Khalifa. Aka bar Aliyu (a) da kuri’u biyu.    Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowaidan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Abdurrahman dan Auf wafatin manzon All tabbatar da cewa daya daga cikin masu sauraro ya nada shi

এছাড়াও পড়ুন:

Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO

Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana damuwa kan sabon harajin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya saka kan kayayyakin da ke shiga da su ƙasar daga ƙasashen duniya.

Wannan haraji ya haɗa har da kashi 14 cikin 100 na kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga Najeriya.

Ɗalibai za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnatin Kano Kakakin APC na Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu

A cewar sanarwar da WTO ta fitar a ranar Alhamis, hukumar na nazari da bibiyar matakin domin fahimtar yadda zai shafi cinikayya da kuma ci gaban tattalin arziƙin duniya.

Okonjo-Iweala, ta ce wasu ƙasashe mambobin WTO sun nuna damuwa kan wannan lamari, inda suka buƙaci ɗaukar matakan rage illar hakan.

Harajin da Trump ya sanar ranar 2 ga watan Afrilu ya zo ne daidai lokacin da ƙasashe da dama ke ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙinsu daga tasirin rikicin Rasha da Ukraine, da kuma tasirin hauhawar farashi da ake fama da shi a duniya.

Me ƙasashe ke cewa kan sabon harajin?

Ƙasashe irin su China da Turai sun nuna rashin jin daɗinsu kan harajin Trump, inda China ta mayar da martani da nata sabon harajin.

A Najeriya kuwa, masana tattalin arziƙi sun fara fargabar cewa ƙarin harajin zai ƙara tsadar kayayyaki da kuma rage damar fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.

Ƙungiyoyin cinikayya sun fara kira ga Amurka da ta janye harajin, domin gudun jefa ƙasashe masu tasowa cikin mawuyacin hali.

Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da Amurka ke cikin yanayin siyasa mai zafi, tun bayan da Trump ya sake ɗarewa karagar mulki a karo na biyu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 106
  • An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 105
  • Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Ia) 104
  • Jinkirin Fansho: PTAD Ta Fadi Dalili, Ta Ce Za a Biya Kudaden Wannan Wata
  • Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO
  • Wata Babbar Kotu A Seoul Ta Tube Shugaban Kasa Daga Mukaminsa Saboda Doka Ta Bacin Da Ya Kafa
  • Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (1)
  • Uromi: Matar Mamaci Ta Haihu Bayan Rasuwar Mijinta, Ta Nemi Taimako