HausaTv:
2025-04-26@12:12:48 GMT

Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Ia) 104

Published: 5th, April 2025 GMT

104- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani  mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.

Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).

A cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda Khalifa na biyu na nada mutane shida, tare da umurnin su zabi daya daga cikinsu a matsayin Khalifan manzon All..(s) a kan al-ummarsa, kuma bayan wafatin umar suna da kwanaki uku da su gudanar da zaben.

Kuma mun bayyana yadda zaben ya kasance. A zaman farko a baitil Malin musulmi a Madina, ko kuma a gidan wani mutum daga cikin mutanen madina wanda ake kira Musauwar dan Mukhramah almakhzumi.

Mun ji yassa Aliyu dan Alitalib (a) ya tashi yayi Magana mai tsawo ya na gargadi da kashedi wa masu zaben 5, da kuma wadanda suke halattan zaman, daga cikin akwai dansa Imam Alhassan (a) da kuma jami’an tsaro wadanda suka yi masu kawanya, da kuma sauran sahabban manzon All..(a), wadanda suka hada da Ammar dan Yasir, da Mughiratu dan Shubah wadanda suka zauna a kofar shiga wurin suna sararo.

Imam Ali(a) ya fada masu cewa, idan ba su zabeshi ba, suka kuma mayar masa hakkinsa, to kuwa ya kafa hujja a kan su, sannan zasu ga abinda ba sa so a cikin Al-ummar musulmi. Daga ciki za su ga yanda wa su zasu nemi wannan kujerar ta Khalifancin manzon All..(s) ta hanyar zubar da jinin musulmi, Kuma zasu ga rarraba a cikin musulmi, sannan zasu ga yadda wasu zasu karya al-kawali don neman kai wa ga wannan kujera mai muhimmanci.

Misali na farko shi ne, bayan an kashe khalif ana uku, wato Uthman dan Affan, kuma mutane suka zabi Imam Ali (a) a matsayin khalifa, sai Mu’awiyya dan abisufyan wanda wali ne a sham, yayi masa tawaye yaki yayi masa bai’a, Sannan a lokaci guda, Talha da Zubair, bayan sun yi wa Imam Ali (a) bai’a a Madina a matsayin Khalifan manzon All..(s) sai suka nemi izininsa kan cewa zasu je Umra, sai suka je makka suka hadu da Aisha matar manzon All..(s), suka ingiza mutane kan khalif ana 4, suka zargeshi da kashe Uthman, suka tara mutane suka je garin Basra, suka kama wali ko gwamnan Imam Ali(a) a Basra suka kulle shi, suka kwace iko da garin, suka kwace dukkan dukiyan baitul malin garin.

Daga karshe Imam Ali(a) ya zo basra ya yakesu, gaba daya sun mutu a wannan yakin, wanda ya tabbatar da zancenta a zaman zaben khalifa na uku kan cewa wasu daga cikin mutanen nan guda 5,  zasu zama shuwagabannin bata da jahiliyya. Sai gashi ya tabbata sune Talha da Zubair.

Sannan ma’awiya ya zare takobi ya yaki Imam (a) a Siffin inda da sunan neman jinin Uthman yana neman Khalifanci wa kansa. Aka zubar da jinin dubban musulmi a yakin.

Sannan daga karshe bayan shahadar Imam Ali (a) Mu’awiya ya kwace khalifanci da karfi daga hannun Imam Hassan (a), sannan bayan haka sai ya tilastawa al-ummar Musulmi yin bai’a ga dansa yazidu. Ya yi watsi da dukkan al-kawulan da yayiwa Imam Hassan(a) na cewa, idan ya mutu ya mayarwa Imam Hassan(a) khalifanci ko kuma kaninsa Imam Hussain(a) idan ya bai da rai.

Wannan ma ya tabbatar da zancen Imam Ali(a) a majalisar shura kan cewa, wadanda basu cancanci zama khalifofi ba, zasu nemeta su kuma zubar da jinin musulmi, su kuma karya al-kawulan da suka dauka don kaiwa ga wannan babban kujera.

Imam Ali(a) ya fada masu a wancan majalisar zaben Khalifa na uku, wasu abubuwan da zasu faru a lokacinda shi zai zama khalifa, na tsawon shekaru 4 da watanni, na yake-yaken da ya yi a lokacin. Da kuma abinda zai faru da Imam Hassan (a), har zuwa zamanin yazid dan Mu’awiya ya zama Khalifam musulmi, suna so ko basa so.

Bayan jawabinda mun ji yadda aka Zabi Uthman dan Affan, bayan da Zubair ya zabi Ali (a), sannan Talha ya zabi Uthman, sannan sa’ad dan Abiwakkas ya zabi Abdurrahman dan Auf,  wanda daga karshe ya zabi Uthman, sai Aliyu (a) ya tashi da kuri’u biyu kacal, Uthman ya tashi da kuri’u hudu, banda haka Abdurraman dan auf ya na  bangaresa.  

A wata ruwaya an bayyana cewa a lokacinda Abdurrahman dan Auf, ya ga cewa lokaci ya kure masa, kowa na jiran matsayin da zai dauka, Aliyu zai zaba ko Uthman, ya tsaya a rikice, yana bukatar a bashi shawara, kuraishwa suka ce masa ya zabi Uthman, haka ma Banu Umayya.

Sai Abdurrahman ya fadawa dan yar’uwarsa, wato Musawwar, ya  kira masa Aliyu da Uthman, sai yace da wa zan fara, sai yace: da wanda kaga dama, sai musawwar ya kawo su, sai  Abdurrahaman ya sake cewa: Ku bani shawara, sai Ammar dan Yasar (daya daga shi’an Ali (a) ya ce masa: Idan baka son mutane su yi sabani a tsakaninsu ka zabi Aliyu(a).

Sai Mikdad dan Aswad shi ma daga cikin shi’ar Ali(a) ya zo ya goyi bayan abinda Ammar dan Yasir ya fada, wato idan kana son hadin kan musulmi ka zabi Aliyu.(a).

Daga nan sai Abdullahi ibn Abisarkh, daya daga cikin shuwagabannin banu Umayyah, ya fadawa Abdurrahman bin Auf. kan cewa: Idan ba ka son kuraishawa su yi sabani a tsakaninsu ka zabi Uthman, sai Abdullahi ibn Abi-Rabi’ah Almakhzumi, ya tashi ya goya masa baya, ya fadawa Abdurrahman dan Auf: idan ka zabi Uthman, zamu ji mu yi biyayya.

Sai Ammar ya tashi ya aibata Abdullahi dan Abi-sarkh, ya ce masa: Yau she kake bukatar musulunci da Alkhairi

Ammar ya yi gaskiya, saboda idan an dubi tarihi, za’a ga cewa, shi wannan Abdullahi dan Abisarkh yana daga cikin wadanda suka cutar da manzon All..(s) kafin fatahin Makka, har sai ya kai ga manzon All..(s), bayan ya kwace Makka a shekara ta 8 bayan hijira, ya ba da umurnin  a kashe  wasu mutane, ko da an samesu rike da rigar dakin Ka’aba. Wanda yake da wannan sabikan ne zai bada shawara kan makomar khalifancin Musulmi?

Sai aka yi ta jayayya mai yawa tsakanin Banu Hashin dangin manzo All..(s) da kuma Banu Umayya, dangin Abu Sufyan, kan wa Abdurrahman dan Auf zai zaba. Daga karshe Ammar dan Yasir ya sake tashi ya yi wa mutanen Magana yana cewa: Ya ku mutnane, Lalleh All..ya daukakaku da annabinsa(a), ya daukakaku da addinsa, har zuwa yauce zaku kauda al-amarin Khalifanci daga Ahlubaitin annabinku?.

A lokacinda jayayya ta yawaita, a cikin mutane, sai Sa’ada ya matso kusa da Abdurrahman dan Auf, ya ce masa, ka kawo karshen wannan jayayyar ka zabi daga daga cikinsu.

A nan sai Abdurrahman dan Auf ya matso kusa da Aliyu dan Abitalib, (a) ya ce masa: Zan maka bai’a a kan riko da littafin All..da sunnar annabi (s) da kuma ayyukan Abubakar da Umar?.

Sai Imam (a) ya ce: Sai dai tare da riko da Littafin All..da sannar manzonsa da kuma intihadina da ra’ayi na.

Wannan shi ne ake tsammanin ya fita daga bakin Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). Wanda baya kodayin zama khalifa ko shugaba don bukatar kansa.  Ta yaya Abdurrahman dau Auf zai shardantawa Aliyu dan Abitalib, bin ayyukan Abubakar da Umar a khalifancin manzon All… bayan da suna sabani a tsakaninsu a cikin al-amura a tsakaninsu?.

Misali Umar ya na ganin Abubakar ya yi kisasi, ko ya kashe Khalid dan Walid wanda ya kashe Malik dan Nuwaira sannan ya tare da matansa a cikin daren da ya kashe mijinta. A yayinda Abubakar yana ganin, khalid ya yi tawili ne ya yi kuskura, don haka an gafarta masa, kuma tunda shi ne Khalifa a lokacin ra’ayinsa ne ya tabbata.

A wasu lokutan ra’ayoyinsu sun sabawa alkur’ani da sunnar manzon All…(s), ta yaya za’a shardantawa Aliyu Dan Abitalib bin ayyukan Khalifofin da suka gabace shi, Al-hali ya fisu sanin Littafin All..da sunnar manzon All..(s)?.

Ta ya ya za’a haramta masa amfani da ra’ayinsa da ijtihadinsa, al-hali ra’ayinsa, ra’ayin Alkur’ani ne, Ra’ayinsa ra’ayin manzon All..(s). Al-hali ra’ayinsa baya sabawa Al-kur’ani da sunnar manzon All..(s)?

A cikin hadisi, manzon All..(s) ya ce: Aliyu yana tare da gaskiya gaskiya tana tare da Ali. A wani hadisin ya ce: Aliyu yana tare da Alkur’ani Al-kur’ani yana tare da Ali.

Wanda ya kasance haka, ta yaya zai bi ayyukan wadanda suke iya yin hukunci sabanin Alkur’ani da sunnar manzon All..(s). Don haka sai Aliyu (a) ya cemasa ‘aa’a.

Sannan idan muka dauki siyasar Abubakar zamu ga cewa: Ta fi kusa da daidaito tsakanin musulmi, sabanin siyasar Umar, wanda ya samar da aji-aji, da fifiko tsakanin musulmi.

A cikin shirye-shiryemmu a baya mun bayyana tsarin khalifa na biyu a rabon dukiya, wanda hakan ya samar da masu arziki sosai a cikin musulmi da kuma wadanda aka haramta masu kome. Suna cikin talauci da rashi, a yayinda wasu kuma suke da hannayen kofofin gidajensu an yi su da karfin zinari.

Sannan Khalifa Umar ya hana auren mut’a, misali a lokacin Khalifancin sa, bayan da wannan auren ayar alkur’aci ya tabbatar da shi, an yi wannan auren a zamanin manzon All..(s) har yayi wafati bai hana shi ba, an yi shi a zamanin Abubakar har yayi wafati bai hana shi ba, sannan an yi shi a zamanin shi Khalifa Umar, bai hana ba, sai lokacinda wani yayi irin wannan auren da wata daga cikin danginsa, sai ya hau mimbarin manzon All..(s) ya fada a fili, kan cewa auren mut’a an yishi a zamanin rayuwar manzon All..da Abubakar, amma ni na hana shi, duk wanda ya sake yinsa sai ya azabtar da shi.

To a wannan halin ta yaya Aliyu (a) zai amince da riko da ayyukan Abubakar da Umar, wadanda suka sabawa juna, sannan wasunsu sun sabawa All..da manzonsa (s)?

Don haka a lokacin da, Abdurrahman dan Auf ya debe kauna daga amincewar Amirul muminina (a) da sharuddan da ya kafa masa, sai ya koma wannan Uthman, bin Affan ya ce masa ya amince da dukkan sharuddan da ya kafa. Sai yayi masa ba’a a aka waste mafi yawan mutane suna cewa Uthman ya sameta, wato Khalifancin. Sunan ta murna.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da sunnar manzon All Abdurrahman dan Auf masu sauraro wadanda suka Daga karshe daga karshe

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe

Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.

 

Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10.

 

Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar.

 

A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen hana barkewar rikici a yankin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan kasuwar da suka ɓoye kayan abinci na tafka asara
  • Sayyid Fadhlullahi Ya Jaddada Muhimmanci Samar Da Makamai Ciki Har Da Kare Kasa Daga Dan Mamaya
  • An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi
  • Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)
  • MDD : ba tabbas kan ko za’a kawar da zazzabin malaria nan da shekarar 2030
  • Jagora: Tafarkin Imaman Ahlul Bayti ( A.S) Na Gwgawarmaya Ne Da Jajurcewa
  • **Gwamnati Za Ta Kwace Gidajen Ma’aikatan Da Suka Yi Ritaya Ba Su Biya Bashin Gidaje Ba
  • Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 113
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 112