Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 105
Published: 5th, April 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).
A cikin shirimmu da ya gabata, mun yi magana kan yadda aka zabi Khalifa na uku Uthman bin Afffan a matsayin khalifa, a dai dais aura kadan lokacinda Khalifa na biyu ya ware-masu na su zabi daya daga cikinsu a sare wuyoyin su.
Abdurrahman dan Auf wanda shi ne shugaban kwamitin ya rasa abinda zai yi, yayi ta neman shawara daga mutane daban daban. Kowa da abinda yake fada masa. Ammar dan Yasir ya ce masa idan yana son hadin kan musulmi to ya zabi Aliyu dan Abitalib(a) . wasu kuma sun ce masa idan yana son hadin kan kuraishawa to ya zabi Uthman dan Affan. Wannan haka ya ci gaba da faruwa, har zuwa lokacinda Sa’ad dan Abi wakkas ya zo kusa ya fada masa cewa ya yi saura a yanke wannan jayayyar ya zabi daya daga cikin wadannan mutane biyu.
A nan ne sai ya zo kusa da Aliyu dan Abitalib (a) yace masa, zan yi maka bai’a tare da sharadin zaka yi hukunci da littafin Allah da sunnar manzon All..da kuma ayyukan Abubakar da Umar. Sai Ali(a) ya bashi amsa da cewa, sai da littafin All..da sunnan Manzon All..da kuma ijtihadi na da ra’ayi na.
Sai abdurrahman yayi kokarin gamsar da shi ya amince da hakan, amma ya ki amincewa. Sai kawai ya koma wajen Uthmanu, ya bijiromasa sharuddan da ya bijirowa Aliyu (a). sai ya ce ka kawota da dukkan sharuddanta na amince. Sai Abdurrahman yayi masa bai’a a matsayin khalif ana hudu.
Aliyu dan Abitalib (a) bai ji dadi ba, sai ya zo ya fadawa Abdurrahman kan cewa yayi wa Uthman bai’a ne don ya mayar masa da ita wata rana, sai yayi addu’a , yana cewa All..kada ya daidaita a tsakaninsu.
Daga nan sai Aliyu (a) ya juya ta fita daga cikin masallaci ko wurin taron. Wannan duk yana faruwa a gaban Imam Hassan (a). Ya ga a wannan karomma yadda aka hana babanshi hakkinsa, wanda All..ya bashi. Daga nan Magana ta kare, Uthman ya zama khalif ana ukku. Amma wani irin shugabancin ne Uthman yayi?
Malaman tarihi da dama sun bayyana cewa uthman ya karbi Khalifanci ne kawai amma ya barwa Marwan dan Hakan dan amminsa kuma surukinsa yana tafiyar da al-amura al-ummar musulmi.
Shugabancinsa na ciki da matsalolin. Banda haka sanadiyyar yadda ya tafiyar da shugabancinsa al-ummar musulmi ta fada cikin matsaloli, kafin a kashe shi da kuma bayan kisansa har zuwa yau shekaru kimani 1400 da suka gabata, musulmi suna dandana, musibar abinda shugabancin Khalifa Uthman ya jawo, kuma har tashin kiyamah.
Matsala ta farko wacce Khalifa Uthman ya fara fuskanta ita ce. Ubaidullah dan Umar dan Khalifa Umar ya dauki makami ya je ya kashe Hurmozan, da Jufainatu da kuma diyar Abu Lulu’a don daukar fansar kissan mahaifinsa Khalifa na biyu. Wadan nan da ya kashe ba sune suka kashe babansa ba, wanda ya kashe babansa shi ne Abu lulu’a shi kuma ya gudu ya bar gari.
Wasu kuma sun ce wasu sahabban manzon All..(s) sun kashe shi, amma babbar matsala ita ce kissan da Ubaidulahi dan Umar yayiwa, Hurmozan, da Jufainah da kuma diyar Abu Lulul’i. don basu da hannu wajen kashe Khalifa Umar.
Har’ila yau wannan kissar ta faru ne kafin a zabi Khalifa na ukku bayan da Abu lulu’I ya soki Khalifa da wuka a masallaci yana bada sallah, kafin a zabi khalif ana uku.
Don haka matsala ta farko wacce ya fuskanta ita ce batun hukuncin Ubaidullah dan Umar, wasu sahabban manzon All..(s) sun dage kan cewa sai an yi kisasi kan Ubaidullah, saboda kissan da gangan ce. Daga cikin wadanda suke da wannan ra’ayin akwai amirulmuminina Aliyu dan abitalib (a).
Don haka Khalifa Uthman ya nemi shawarar sahabban manzon All..(s) da dama, wasu suce ya yi kisasi wasu kuma su ce ya biya diyya, wasu sun ce masa ta yaya zai kashe dan Khalifa Umar a yau bayan an kashe babansu a jiya. Wasu kuma sun ce masa a wajen yin kisasi shi ya dace, don kada wani dan babban gida ya sake irin wannan, ya zama idan mutum ya fita daga gidan babban mutum sai a ki yi masa hadda, amma in dan talaka ne sai a zartar da haddi a kansa, da sauransu.
Amma Amru dan Asi ya bashi shawara kan cewa.:
A lokacinda ubaidulla kashe wadannan mutane, kai ba khalifa bane, don haka kada ka sa kanka cikin matsala, kayi duk abinda zaka yi da shi in banda kisa.
A nan khalifa ya karbi shawarar dan Ass, ya ce zai biya diyyar kissan Hurmuzan, daga cikin kudinsa ba na Baitul mali ba, sannan ya bada umurnin a saki Ubaidullah dan Umar wandakafin haka ana tsare da shi a gidan yari.
Amma wasu sahabban sun ci gaba da yi masa barzana kan cewa duk sanda aka sami dama sai an zartar da haddin kisasa a kansa.
Daga cikinsu akwai Ziyad dan Lubaid, wanda Ubaidullah ya kai kararsa gaban Khalifa, uthman wanda ya kira shi ya kuma ce masa kada ya sake.
Daga karshe dai Khalifa ya ce masa ya bar madina ya koma Kufa da zama, ya bashi gida a can har lokacinda al-amura zasu lafa. Da haka aka wuce maganar Ubaidullah dan Umar.
Malaman addinin musulunci a tsawon tarihi sun yi ta sabani a tsakaninsu dangane da yadda Khalifa na uku ya warware maganar kissan Hurmuzan da Juhainatu da kuma diyar Abu lulu’a a farkon khalifancinsa.
Wasu suna ganin alkawalin da Khalifa Uthman ya dauka daga Abdurrahman dan Auf na cewa za iyi hukunci da littafin All..da sunnar manzon All…(s), ya sabawa masu a hukunci na farko da yayi a farkon Khalifancinsa.
Suna kafa hujja da hadisin manzon All..(s) wanda yake Magana a kan zartar da haddin All..a kan talaka da masu arziki, kuma ya nuna masu a aikace kan wani ko wata da tayi sata kuma wanda ya fito daga babban gida. Don haka ya zartar da hukunci All..a kanta. Sannan yace.. da Fatimah(s) diyar Muhammadu (s) zata yi sata da ya yanke hannunta.
Amma Taha Hussain sanennen marubuci dan kasar Masar ya na ganin a wannan halin, matakin da khalifa Uthman ya dauka shi ne dai dai, don a musulunci manzon All..(s) ya bada umurnin a yi watsi da haddi ko da da Shubha ne, yace ana iya daukar shubaha a nan kasancewar ubaidullahi dan Umar yana cikin fushi a lokacinda ya kashe wadannan rayuka guda uku.
Amma idan mun dawo kan Imam Hassan (a) a zamanin Khalifa Uthman, zamu ga cewa a lokacin shi matashi ne dan shakara kimani 20 a duniya. Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, Imam Hassan (a) ya je yaki karkashin rundunar Ukbatu dan Nafiu, da Abdullahi dan Nafiu, zuwa afrika kuma sun sami nasara yada fadada daular musulunci a lokacin har zuwa mafi yawan arewacin Afrika.
Sannan daga baya Abdullahi dan Abisarkh ya nemi izinin Uthman ya kara fafada daular musulunci a arewacin Afirka, sai ya bashi izini, ya kuma kara masa sojoji. Abdullahi dan Abisarkh ya fadada daulara a wasu yankuna.
Wasu malaman sun bayyana cewa a cikin rundunar Akwai, Amr dan Ass, Abdullahi dan Jaafar, da Alhassan da Alhussain (a). kuma sun sami nasara a yankin.
Hakama sun fito yaki zuwa Tabriztan a cikin kasar farisa a lokacin ina shima suka sami nasara.
Sai dai akwai wasu malamai suna musanta cewa Imam Alhassan da Imam Alhussain sun je yaki fadada daular musuluni a zamanin khalifa Uthman kamar yadda muka ambata.
Hakama marubucin littafin futuhatul Islamiyya, bai kawo labarin cewa Alhassan da Alhussain (a) sun je yake-yaken futuhat a zamanin khalif ana ukku a arewacin afrika ba. Amma ya kawo cewa sun halacci yakin Tabristan na kasar Farisa a lokacin.
Ynazun kuma sai siyasar dukiya a zamanin khalifa na uku, wanda yake da bambanci so sai idan an kwatanta da wadanda suka gaba ceshi. Khalifa na farko ya ci gaba da raba kudi kamar yadda manzon All..(s) yake yi a mafi yawan lokuta. Amma khalifa na biyu shi ne ya samar da matakai-matakai a tsakanin musulmi, kamar yadda muka fada a baya.
Asalin rabon kudi a musulunci, kamar yadda Amirulmuminina (a) ya fadawa Abdullahi dan Zam’ah a lokacinda ya zo masa a lokacin khalifancinsa.yace masa (wannan dukiyar nan aka b aba nawa bane, wannan dukiyar na musulmi ne, wanda takubbansu suka samar da su, idan ka yi tarayya da su a yakin da suka yi, kaima kana da rabo kamar yadda suke da shi a cikinsa, in ba haka ba, abinda suka samar ba zai zama rabon waninsu ba.).
Banda haka ya rubutawa walinsa a Makka Kathum ibn Abbas, y ace masa: ka duba cikin abinda ka tar ana dukiya, ka raba shi cikin wadanda suke da iyali mai yawa, da kuma wadanda suke fama da yunwa. Ka tabbatar da cewa ka bawa wadanda suke fama da talauci …sannan abinda ya rage ka aiko mana don mu rabawa wadanda suke wajemmu..
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan all..ya kaimu wassalamu alaikum warhamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Ubaidullah dan Umar Khalifa Uthman ya khalifa Uthman ya wadanda suke wasu kuma su masu sauraro kamar yadda
এছাড়াও পড়ুন:
Ƙoƙarin Tsige Sanata Natasha Ya Gaza Cika Ƙa’idar Doka – INEC
Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa takardar neman tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ba ta cika sharuɗɗan doka da kundin tsarin mulki ya tanada ba.
INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa takaitacciya da ta wallafa a shafinta na Facebook yau Alhamis, tana cewa: “Takardar neman tsige Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya ba ta cika sharuɗɗan da ke cikin sashi na 69(a) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ba.”
INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata NatashaSai dai hukumar ta yi alƙawarin fitar da cikakken bayani kan wannan ci gaba nan ba da jimawa ba.
Rahoton wakilinmu ya nuna cewa har yanzu ba a tabbatar ko masu ƙorafin za su samu damar gyara takardar domin dace wa da doka ko kuma za a yi watsi da ita gaba ɗaya ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp