Aminiya:
2025-04-27@03:32:37 GMT

An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe

Published: 5th, April 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, ta ceto fasinjoji 14 da wasu ’yan bindiga suka sace yayin da suke tafiya a kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo.

Sai dai uku daga cikin fasinjojin sun rasu, ciki har da direban motar.

Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO Ɗalibai za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnatin Kano

A cewar sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Catherine Anene, ta fitar a ranar Juma’a, lamarin ya faru ne a ranar 3 ga watan Afrilu, 2025.

Wasu ’yan bindiga sun farmaki motar a yankin Otukpo Burnt Bricks, inda suka buɗe wa direban da wani fasinja da ke gaba wuta, lamarin da ya tilasta direban tsayawa.

’Yan sanda tare da jami’an tsaro sun isa wajen da abin ya faru cikin gaggawa.

Sun iske direban da wani fasinja a cikin mota kwance cikin jini, amma an garzaya da su asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsu.

’Yan bindigar sun yi awon gaba da sauran fasinjojin zuwa cikin daji.

A ranar 4 ga watan Afrilu, ’yan sanda sun bi sahunsu zuwa cikin dajin inda suka yi musayar wuta, wanda hakan ya sa suke tsere suka bar mutanen da suka sace.

Biyu daga cikin waɗanda aka sace an yi musu rauni da adda kafin a ceto su.

An samu nasarar ceto mutum 14, amma ɗaya daga cikinsu ya rasu a asibiti, sauran kuma suna karɓar magani.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Steve Yabanet, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu, kuma ya sha alwashin kamo maharan.

Ya kuma buƙaci al’ummar Otukpo da su kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbin bindiga, domin an jikkata wasu daga cikin ’yan bindigar yayin artabu da jami’an tsaro.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Yan Sanda yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Musanta Zargin Nethalands Na Cewa Tana Da Hannun A Kokarin Kisa A Kasar

Ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Netherlands ta yi watsi da zargin da gwamnatin kasar takewa JMI na kokarin aiwatar da kashe-kashe har guda biyu a shekarar da ta gabata.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tace Ofishin jakadancin Iran da ke Netherlands  ta fidda wannan sanarwan ne a jiya Alhamis. Ta kuma kara da cewa, kasar Iran wacce ta fi ko wace kasa a duniya fama da yan ta’adda, ba za ta yi kokarin kasashe wani a wani wuri ba.

Sanarwan ta bayyana cewa wannan al-amarin siyasace ta tsakanin jami’an siyasa na kasar ta Netherlands  don neman amincewar masu kuri’a.

Kafin haka dai wata cibiyar ayyukan tsaro ta kasar Netherlands  mai suna AIVD ta bada rahotomta na shekara shekara kan abinda ya shafi ayyukan ta’addancin inda ta ammabi kasar Iran a ciki.

Har’ila yau wannan rahoton yasa ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Netherlands  ta kira jakadan JMI a kasar zuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar don gabatar da korafinta.

Gwamnatocin kasashen Turai musamman kasar Faransa tana gudanar da taron yan adawa da JMI a kasashensu, wadanda kuma sune suka kashe Iraniyawa da dama a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a kasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yan Gudun Hijiran Sudan Sun Yi Kira Ga Kungiyoyin Kasa Da Kasa Da Su Ceto Yara Da Tsofaffi Daga Mummunan Kangi A Sudan
  • ‘Yan Bindiga Na Kakaba Harajin Miliyoyin Naira Ga Mutanen Zamfara
  • An kashe Shugaban coci da wata mace a Benuwe
  • An sako limamin Katolika da aka sace a Kaduna
  • Iran Ta Musanta Zargin Nethalands Na Cewa Tana Da Hannun A Kokarin Kisa A Kasar
  • Kudaden Da Ke Hannun Mutane Sun Ragu Zuwa Naira Tiriliyan 5 – Rahoto
  • Darussa Daga Tafsirin Ramadan Daga Masu Bibiya (4)
  • Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira A Ranar Juma’a A Maiduguri
  • An Umurci Sojoji Su Kawarda ‘Yan Bindiga Daga Kwara Da Niger A Cikin Wata Daya
  • 2025: NAHCON Ta Ware Kujerun Aikin Hajji 1,407 Ga Jihar Taraba