Bruno Fernandes Ba Na Sayarwa Ba Ne – Ruben Amorim
Published: 5th, April 2025 GMT
Babban kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ruben Amorim ya ce ya shaida wa Bruno Fernandes cewa ba zai bar shi ya bar kungiyar ba a bazara, kyaftin din kungiyar Fernandes wanda ya rattaba hannu a kan kwantiragin har zuwa 2027 a watan Agustan da ya gabata ya kasance tauraron dan wasan United a kakar wasa ta bana.
Bruno Fernandes ya ci kwallaye 95 a wasanni 277 da ya buga tun zuwansa Manchester United daga Sporting a shekarar 2020, a karshen mako rahotanni sun bayyana ana danganta dan wasan mai shekaru 30 da komawa Real Madrid.
Spain Ta Lallasa Ingila A Wasan Ƙarshe Na Kofin Euro 2024 De Bruyne Zai Bar Manchester City A Ƙarshen Kakar Wasanni“A’a, ba zai faru ba,” in ji Amorim, lokacin da aka tambaye shi game da jita-jita a wani taron manema labarai kafin buga wasa a gasar Premier ranar Talata da Nottingham Forest, da aka tambaye shi ta yaya zai tabbata haka, tsohon kocin na Sporting ya kara da cewa: “Ba zai je ko’ina ba saboda na riga na fada masa'”.
Fernandes ya zura kwallaye 16 a dukkan gasa a kakar wasa ta bana yayin da babu wani dan wasan United da ya jefa adadin wadannan kwallaye a bana, a mako na karshe kafin hutun kasa da kasa na baya-bayan nan, Fernandes ya zura kwallaye biyar, ciki har da ha-trick a gasar cin kofin Europa da suka doke Real Sociedad.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Fara Binciken Ƙwaƙwaf Kan Yaddda NNPCL Ke Hada-hadar Kuɗaɗensa – Ministan Kuɗi
“Akwai wasu bincike da ake gudanarwa domin kamar yadda muka sani, an sanar da cire tallafin man fetur ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023, amma an dauki lokaci kafin a cimma wannan kudurin. A halin yanzu, wani bangare na biyan basussukan da ake bin NNPC, daga kasafin kudin gwamnati ake tanada”.
Ya kara da cewa, babban aikin da ke gaban NNPCL shi ne bunkasa hako danyen mai da kuma samar da karin kudaden shiga – a takardun Dala zuwa Asusun Tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp