Aminiya:
2025-04-06@04:44:45 GMT

Rashin tsaro a Filato ya wuce rikicin manoma da makiyaya – Muftwang

Published: 5th, April 2025 GMT

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya ce hare-hare da kashe-kashen da ake yi a wasu sassan jihar wasu ne ke ɗaukar nauyinsu ba rikicin manoma da makiyaya ba ne.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bikin baje kolin kayayyaki da fasaha da ƙungiyar Tincity Fashion Week ta shirya a daren Juma’a a Abuja.

An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya bayar da rahoton cewa, a ranar 2 ga watan Afrilu, wasu ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Manguno, Daffo da Josho na ƙaramar hukumar Bokkos  ta jihar.

Maharan sun kashe mutane da dama tare da lalata gidaje da wasu kadarori na miliyoyi.

Mutfwang, wanda ya jaddada cewa hare-haren an tsara shi ne, ya yi alƙawarin cewa gwamnati da hukumomin tsaro sun tanadi matakan daƙile afkuwar lamarin nan gaba.

“Ina so in gode muku da kuke nan domin goyon bayanku da kuma karrama Filato tare da halartarku a wannan taron, ba mu ɗauki wannan haɗin kai da wasa ba.

“Mun yi tunanin dakatar da wannan taron ne saboda yanayin tsaro da jihar ke fama da shi, amma mun yanke shawarar kada lamarin ya lalata mana kyawawan abubuwan da ya kamata mu yi na taron biki.

“Kuma dole ne in ce manufar maƙiya ita ce jefa jihar cikin ruɗu da baƙin ciki, amma za mu kauda  manufarsu ba za mu ba damar yin abin da suke so ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Caleb Mutfwang

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi

Hedikwatar ’yan sandan Nijeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II domin amsa tambayoyi kan wani lamari da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano.

A baya dai rundunar ’yan sanda tare da sauran wasu jami’an tsaro a jihar sun soke duk wani hawan bikin Sallah, musamman jerin gwanon dawakai a jihar, saboda dalilan tsaro.

Motar fasinja ta kama wuta wasu sun tsallake rijiya da baya Rashin tsaro a Filato ya wuce rikicin manoma da makiyaya – Muftwang

Sai dai a yayin da Sarkin ke tattaki domin halartar Sallah a filin Idi na Ƙofar Mata a ranar 30 ga watan Maris, an caka wa wani ɗan banga da ke kare Sarkin wuƙa har lahira, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Bayan faruwar lamarin, wasu sun shaida wa majiyar Daily Nigerian cewa tun da farko babban Sufeton ’yan sandan ƙasar, Kayode Egbetokun ya umarci Kwamishinan ’yan sandan jihar da ya kama sarkin.

Kamar yadda aka samu rahoto, Kwamishinan ya bayyanawa Sufeto Janar ɗin cewa, lamarin ba shi da alaƙa da keta dokar hana hawan Sallah, kuma Sarkin bai yi amfani da dawakai wajen ziyartar gidan gwamnati ba kamar yadda al’adar ta tanada.

Sufeta Janar ya umurci sashen leƙen asiri na rundunar da ta karbe fayil ɗin ƙarar tare da gayyatar Sarkin zuwa Abuja domin amsa tambayoyi.

A wata wasiƙar gayyata da ya sanya wa hannu Kwamishina ’yan sanda CP Olajide Ibitoye, sun gayyaci sarkin da ya gurfana a gaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar a ranar Talata 8 ga Afrilu da ƙarfe 10 na safe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rashin ɗa’a: Gwamnatin Borno ta gargaɗi masu amfani da shafukan sada zumunta
  • ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi
  • Al-Houthi: Hare-haren Amurka sun kasa dakatar da gwagwarmayar Yeman
  • Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52
  • Gwamnatin Kwara Ta Bullo Da Shirin Habbaka Kiwon Dabbobi Da Raya Karkara
  • Aljeriya ta bukaci taron gaggawa a kwamitin tsaro kan Falasdinu
  • ‘Yan Bindiga A Ƙarƙashin Jagorancin Turji Sun Kashe Manoma 12 A Sokoto
  • Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato
  • Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang