Motar Fasinja ta kama wuta wasu sun tsallake rijiya da baya
Published: 5th, April 2025 GMT
Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar.
Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin Ikorodu tana kan hanyar zuwa CMS a lokacin da lamarin ya faru.
Ya zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoton, masu bayar da agajin gaggawa da suka haɗa da jami’an ’yan sandan Nijeriya, da hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA), da jami’an kashe gobara da jami’an tsaro na yankin, sun isa wurin domin shawo kan gobarar.
Ɗaya daga cikin fasinjojin motar ta shaida wa majiyar cewa gobarar ta tashi ne a matsayin hayaƙi daga ɓangaren direban.
A cewarta, tun farko fasinjojin sun yi tunanin hayaƙin ya fito daga wasu motocin bas ɗin; duk da haka, ba da daɗewa ba hayaƙin ya ƙara tsananta, hakan ya sa su cikin yanayin firgita.
“Da muka ga hayaƙin ya yi yawa, nan take muka fito daga motar bas ɗin kafin wutar ta tashi”, ta ƙara da cewa babu wani daga cikin fasinjojin da ya samu wani rauni.
Ta ƙara da cewa direban motar ya gudu bayan tashin gobarar.
“Direban da kwandastan sun gudu, ba su ma jira su ga abin da zai same mu ba.
“Tabbas, sun san abin da ya faru, sun san motar bas ɗin ba ta da kyau kafin su saka fasinja su bi hanya kuma sun jefa rayuwarmu cikin haɗari,” in ji ta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gobarar bas
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci Kasashen Indiya Da Pakistan Da Hada Kai Don Yakar Ta’addanci
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya bayyanawa firai ministocin kasashen Indiya da Pakistan a maganar da yayi da su ta wayar tarho a jiya Asabar, kan cewa mu hada kai gaba daya don yaki da ayyukan ta’addanci a yankin.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pezeshkiya yana fadawa shuwagabannin kasashen biyu, kan cewa akwai bukatar hada kai tsakanin kasashen biyu da sauran kasashen yankin don yi ki da ayyukan ta’adanci.
Shugaban ya kara jaddada yin allawadai da hare-heren da aka kai cikin kasar Indiya a makon da ya gabata. Ya kuma jajantawa Narendra Mudi firai ministan kasar kasar ta India. Harin dai yan bindiga a garin Pahalga na yankin Kashmir dake karkashin ikon kasar Indiya suka kai, hare-hare kan wasu yan yawan shakatawa wuta sun kuma kashe akalla mutane 27. Tun lokacin ya zuwa yanzu dai sojojin kasashen biyu sun yi musayar wuta a tsakaninsu.