Sojojin Sudan suna ci gaba da bata-kashi da dakarun rundunar kai daukin gaggawa a yammaci da kudancin birnin Umdurman.

Majiyar gwamnatin Sudan ta fada wa manema labaru cewa; An dauke mazauna yankin da ake fadan a birnin Umdurman da adadinsu ya kai 5,000 zuwa arewacinsa.

A lokaci daya kuma sojojin na Sudan suna  ci gaba da abinda su ka kira da “Shara” a yankin “Jabalul-Auliya” dake kudancin birnin Khartum.

A can birnin Al-Fasha, jiragen saman sojojin Sudan suna kai hare-hare akan  wuraren dakarun kai daukin gaggawa a cikin birnin, da hakan ya haddasa asarar ta rayuka da kuma kayan yanki.

A cikin kwanakin bayan nan sojojin Sudan suna samun nasara akan dakarun kare daukin gaggawa da ya hada da korarsu daga birnin Khartum da wasu muhimman birane da su ka hada da Jazira.

Tun a cikin watan Aprilu na 2023 ne dai kasar Sudan ta fada cikin yakin basasa, bayan da dakarun rundunar kai daukin gaggawa su ka mamaye wasu cibiyoyin gwamnati.

 Ya zuwa yanzu dai adadin wadnada su ka rasa rayukansu sun wuce 20,000, yayin da wasu miliyan 15 su ka zama ‘yan hijira.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: daukin gaggawa

এছাড়াও পড়ুন:

Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman da makamai masu linzami

Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama.

Kakakin Rundunar sojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree ya tabbatar da cewa, sojojin Yaman sun gudanar da wani shiri na soji na hadin gwiwa, inda suka yi arangama da jirgin ruwan Amurka Harry Truman da jiragen yakin da yake dauke da su  a arewacin tekun Bahar Maliya.

Saree ya ci gaba da cewa, a harin an yi amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka, kuma harin ya cimma nasara kamar yadda aka tsara, inda ya ce an dauki tsawon sa’o’i da dama ana gudanar da farmakin, kamar yadda kuma a lokaci guda sojojin Yeman sun dakile wani bangare na harin Amurka.

Ya kuma kara tabbatar da cewa dakarun na Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan dukkanin jiragen ruwan yakin Amurka da kuma jiragen da suka keta dokar hana shiga yankunan da aka ayyana, yana mai bayyana cewa wadannan hare-haren wuce gona da iri na Amurka ba za su hana su cika alkawarin da suka dauka na tallafawa al’ummar Palasdinu ba.

Saree ya tabbatar da cewa sojojin Yeman na ci gaba da gudanar da ayyukansu a cikin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, kuma ba za su gushe ba har sai an dakatar da kai farmaki a kan Gaza tare da kawo karshen killacewar da ake yi wa al’ummar yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Faifan bidiyo ya fallasa kisan gillar da Isra’ila ta yi wa likitoci  a Gaza
  • Kwamandan Dakarun RSF Na Sudan Ya Tabbatar Da Janyewarsu Daga Khartoum
  • ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi
  • Saboda Rikicin Kasar Sudan Ta Kudu Shugaba Musaveni Ya Isa Birnin Juba
  • Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno
  • Turji ya kusa komawa ga mahallici –  Sojoji
  • Dakarun Yemen Sun kai hari kan jirgin ruwan yaki na Amurka USS Harry Truman da makamai masu linzami
  • Kungiyar Malaman Musulmi ta yi kira da a dakatar da kisan kiyashi a Gaza cikin gaggawa
  • Aljeriya ta bukaci taron gaggawa a kwamitin tsaro kan Falasdinu