Kungiyar Malaman Musulunci Ta Duniya Ta Yi Fatawar Wajabcin Taimakawa Falasdinawa
Published: 5th, April 2025 GMT
A wata sanarwa da kungiyar ta malaman addinin musulunci ta duniya ta ce wajibi ne akan kowane musulmi wanda yake da iko a fadin duniyar musulunci da ya taimakawa mutanen Gaza da makamai da kayan yaki domin dakile ta’addancin Isra’ila da yake cigaba.
A jiya Juma’a ne kungiyar malaman addinin musuluncin ta duniya ta fitar da wannan fatawa wacce ta kunshi yin kira ga daidaikun musulmi da kuma gwamnatocinsu da su bai wa kungiyoyin gwgawarmaya makamai da kayan yaki da kuma bayanai na sirri akan abokan gaba.
An gina fatawar ne akan cewa matakin farko na wajabcin jihadin akan al’ummar Falasdinu, sannan kasashen dake makwabtaka da Falasdinu da su ka hada Masar, Jordan da kuma Lebanon, sannan kuma dukkanin kasashen larabawa da musulmi.
Har ila yau Fatawar ta yi kira ga musulmin da su yunkura cikin hanzari ba tare da ba ta lokaci ba ta fuskokin soja, tattalin arziki da kuma siyasa.
Sanarwar ta kuma ce, bayan kashe mutane fiye da 50,000 babu makawa a dakatar da wannan kisan kiyashi da kuma barna mai girma da take faruwa.
Kungiyar malaman musulmin duniya ta kuma kira yi kasashen musulmi da suke da alaka da Isra’ila da su yanke ta.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
A soma laluben watan Zhul Qi’da — Sarkin Musulmi
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Zulki’ida na shekarar 1446 daga gobe Lahadi, 29 ga watan Shawwal, wanda ya yi daidai da 27 ga watan Afrilun 2025.
Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa majalisar Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaid ya raba wa manema labarai.
Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanarwa hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi.
A ƙarshe sanarwar ta ce Sarkin ya roƙi Allah Ya kawo wa Nijeriya zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.