HausaTv:
2025-04-26@22:43:57 GMT

Francesca Albanze: Abinda Yake Faruwa A Gaza Kisan Kiyashi Ne

Published: 5th, April 2025 GMT

Wakiliyar musamman ta MDD akan Falasdinu Francesca Albanze ta sanar da cewa; Bayanan da jaridar ” New York Times”  masu kunshe da hotuna na laifin kashe masu aikin ceto a Rafah, suna dakile riwayar Isra’ila.”

Wakiliyar ta MDD ta fada wa tashar talabijin din Aljazeera cewa, abindaya faru kisan kiyashi ne’ sannan ta kara da cewa sojojin Isra’ilan suna yin abinda suke yi ne a tsare,kuma duniya ta yi shiru.

Jaridar “New York Times” ta watsa faifen bidiyo dake dauke da muryar wani ma’aikacin agaji wanda daya ne daga cikin wadanda aka sami gawawwakinsu a cikin wani babban kabari a yankin Rafaha. Bidiyon ya nuna yadda sojojin Isra’ila su ka kai wa  masu aikin agaji hari da gangan, sun kuma san cewa su ne saboda alamomin da suke tattare da su.

Riwayar da HKI ta watsa ita ce, cewa motocin masu aikin agajin sun nufi inda sojojinsu suke ne gadan-gadan cikin shakku.”

Wakiliyar MDD ta kuma kara da cewa; wannan laifin da HKI ta tafka bai kamata a kalle shi nesa da sauran laifukan da take aikatawa ba a Gaza, tana mai kara da cewa; Tun 2023 take yi wa al’ummar Gaza kisan kiyashi a tsare.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Amurka Ya Ce: Natenyahu Ba Zai Hadi Fada Da Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ba

Shugaban Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan Isra’ila Netanyahu ba zai ja shi zuwa shiga cikin yaki da Iran ba, kuma a shirye yake ya gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci da shugaban kasar Iran

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya jaddada cewa: Ba za a sanya shi shiga yaki da Iran ba saboda manufofin fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Trump ya kara da cewa a wata hira da ya yi da mujallar Time, a shirye yake ya gana da Jagoran juyin juya halin Musulunci ko kuma shugaban kasar Iran.

Duk da imanin da ya yi cewa: Amurka da Iran za su iya cimma yarjejeniya, amma Trump ya sake nanata barazanarsa na cewa idan ba a cimma matsaya ba, to zai bi sahun ‘yan yahayoniyya wajen kai wa Iran hari, domin ganin cewa, Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.

Trump ya kuma musanta yunkurin cewa zai hana Isra’ila kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
  • Muhimman Dalilan Kirkiro Da Shirin Inganta Aikin Noma ‘SAPZ’
  • Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina  Cikin Masifar Yunwa
  • An Gano Naira Miliyan 27.8 Da Suke Zirarewa A Albashin Kano
  • Shugaban Amurka Ya Ce: Natenyahu Ba Zai Hadi Fada Da Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ba
  • Duniyarmu A Yau: Shiri Kasashen Yamma Na Kashe Dukkan Falasdinwa A Gaza
  • Sharhin Bayan Labarai: Shin Kissan Mutanen Gaza Gaba Daya
  • Sojan HKI Ya Halaka A Gaza
  • Gwamnatin Haramtacciyar Isra’ila Tana Azabtar Da Falasdinawa A Gidajen Kurkukunta
  • 2025: NAHCON Ta Ware Kujerun Aikin Hajji 1,407 Ga Jihar Taraba