HausaTv:
2025-04-06@11:02:54 GMT

Adadin Shahidan Gaza Sun Kai 50,669

Published: 5th, April 2025 GMT

Ma’aikatar kiwon lafiyar Falasdinawa ta sanar da cewa adadin shahidai a yankin na Gaza sun kai 50,669, yayin da wadanda su ka jikkata su ka kai 115,225.

Dangane da rahoton akan shahidan da ake samu a kowace rana kuwa,ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa ta ce, a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata an sami shahidai 60, wadanda su ka jikkata kuwa sun kai 162.

Sanarwar ta kuma kara da cewa, da akwai wani adadin na shahidai masu yawa da suke kwance a kasa, ba a iya daukarsu balle a yi musu jana’iza ba, saboda yawansu, da kuma wadu dubbai da suke a karkashin baraguzai na gidajen da makaman HKI su ka rusa da mutane a cikinsu.

 A wani labarin daga Gaza, jiragen yakin HKI sun kai hari akan wata rumfa ta raba abinci ga Falasdinawa da suke fama a yunwa, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane 3 a sansanin Khan-Yunus dake kudancin zirin Gaza.

Haka nan kuma sojojin na HKI sun kai hari akan gidajen mutane a cikin gain na Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar muutm guda.

Wasu yankunan da ‘yan sahayoniyar su ka kai wa hare-hare sun hada  Qaizan Abu Rashwan dake kudu masu yammacin Khan-Yunus, da Hayyuz-Zaitun da kudu maso gabashin Gaza, sai kuma titin Sakkah a wannan  birni.

A gefe daya mutanen Gaza suna ci gaba da yin hijirar da aka tilasta su daga Hayyul-Shuja’iyyah, zuwa yammacin Gaza.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52

Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato ya kai 52 kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.

Hakan ya biyo bayan sake gano wasu gawarwaki 40 ne a ranar Laraba da Alhamis da daddare yayin da masu aikin ceto suka ci gaba da kutsawa cikin dazuka don nemo waɗanda suka ɓata.

Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi

Shugaban Ƙungiyar al’adu ta Bokkos Cultural Development Council (BCDC) Vanguard, Farmasum Fuddang, ya shaidawa tashar Talabijin Channels cewa an yi jana’izar mutane 31 a ranar Alhamis tare da wasu  yara biyar da suka ƙone ƙurmus a ƙauyen Hurti. An kashe wasu 11 a ƙauyen Ruwi, huɗu a ƙauyen Manguna tare da kashe mutum ɗaya a ƙauyen Daffo.

A cewar Ƙungiyar al’adu ta Vanguard, mazauna garin na jiran sakamako daga ci gaba da bincike da ceto mutanen da suka ɓata a ƙauyukan Hurti da Mbar.

Gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da hare-haren tare da yin kira da a kwantar da hankula saboda a halin yanzu ana ci gaba da ɗaukar matakan tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, kwamishiniyar yaɗa labarai da sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap ta bayyana damuwarta game da sabbin hare-haren.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu
  • Sharhin Bayan Labarai: Amurka Ba Zata Taba Zama Mai Kawo Karshin Yaki A Gaza Ba
  • Francesca Albanze: Abinda Yake Faruwa A Gaza Kisan Kiyashi Ne
  •  Kungiyar Malaman Musulunci Ta  Duniya Ta  Yi Fatawar Wajabcin Taimakawa Falasdinawa
  • Adadin mutanen da suka mutu a girgizar kasa a Myanmar ya karu zuwa 3,354
  • Sayyid Husi: Hare-haren Amurka Ba Za Su Yi Tasiri Akan Karfinmu Ba
  •  Falasdinawa 86 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Da Su Ka Gabata
  • Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta