Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 106
Published: 6th, April 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan.
///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s).
A cikin shirimmu da ya gabata mun maganar matsala ta farko wacce Khalifa na uku, wato Uthman bin Affan ya fara fuskanta bayan a zabe shi a matsayin Khalifan musulmi. Kuma ita ce batun kissan da Abidullahi dan Umar, dan Khalifa na biyu yayiwa Khurmazan, da Hunaifatuh da kuma diyar Abu Lulu’a wanda ya kashe mahaifinsa Khalifa na biyu.
Dangane da wanda ya kashe shi, malamai da dama sun ce wasu sahabban manzon All..(s) sun kasheshi jim kadan bayan ya soki Khalifan da wuka yaya kokarin kudu. Amma zuwan da Ubaidullahi dan Umar yayi, ya zare takobi ya kashe diyarsa, ya kuma kashe yan kabilarsa guda biyu, wato Farisawa, Khumuzan da kuma Hunaifah, bay a bisa ka’ida, don basu da hannu a cikin kissan mahaifinsa.
Mun je cewa ya zare takobinsa yaka ta kashe mutane, sai da sa’adu dana bi wakkas ya je ya kwace takobi a hannunsa, ya kuma sa aka jefa shi a gidan yari.
Mun yadda sahabban manzon All..(s) da dama suka bukaci Khalifa ya yi masa haddin kisashi. Wato a kashe shi, shima. Amma dangin khalifa na biyu, sun bukaci khalifa ya karbi diyya, don bazasu yi hakurin, an kashe khalifa a gidansu, a jiya, sannan a yau a kashe dansa.
Daga karshe mun ji cewa Khalifa ya karbi shawarar Amru dan Asi, wanda ya ce masa: Ubaidullahi ya aikata wadan nan kashe-kashe ne bayan kissan mahaifinsa Khalifa na biyu, a dai dai lokacinda ba’a zabi Khalifa Uthman a matsayin Khalifa ba, don haka ya ce masa, a yi duk abinda za’a yi amma kasa ya kashe shi.
A nan sai Khalifa Uthman ya zabi ya biya diyya daga kudinsa ga iyalan wadan nan musulmi farisawa. Sannan ya sa aka saki Ubaidullah daga gidan kaso. Amma saboda wasu sahabban sun matsa masa, khalifa ya ce ya koma kufa da zama har zuwa lafawar al-amarin. Ya kuma bashi gida a Kufa.
Bayan haka mun ji yadda Khalifa ya tura rundunoni zuwa arewacin Afirka da kuma Tabrisatan, wadanda suka kara fadada daular musulunci a wadannan yankuna, sannan Imam Hasan da Al-Hussain (a) suna daga cikin wadanda suka je wadan nan yake-yake, wadanda aka sami nasara a cikinsu. Sai dai akwai wasu malaman da suke musanta cewa wadannan Limamai biyu masu tsarki sun je yakin karkashin khalifa na uku da kwamandojinsa.
Banda haka mun yi maganar cewa rabon dukiya a ddinin musulunci a fili yake, manzon All..(s) ya yi an gani, sannan khalifofin da suka zo bayansa, sun yi an gani, inda muka bayyana khalifa na farko bai sauya sosai a kan na manzon All..(s) ba, amma Khalifa Umar shi ya samar da aji a cikin musulmi bayan rabon duniya da dai-dai kamar yadda manzon All..(s), wanda hakan ya yawaita talakawa a cikin musulmi. Amma khalifa na uku, yayi nesa da wadanda suka gabaceshi suka yi.
Wannan hakan ya jawo masa matsaloli har sai da bayan wani lokaci musulmi suka yi masa bore suka kuma kashe shi.
Tsarin rabon dukiyar Khalifa Uthman, tsari ne wanda ya fifita danginsa banu Umayya kan dukkan musulmi, al-hali danginsa banu umayya sune suka fi kowa nuna adawa ga musulunci a jahiliyya, Aliyu ya kashe da dama daga cikinsu a yake-yaken Badar da Uhudu.
01-Abusufyan. Ko way a san cewa Abu sufyan ne ya jawo yakin Badar, amma bai halarci yakin ba, saboda yana rike da dukiyoyin mushrikai a lokacin zuwa Makka. Sannan shi ya jagoranci yakin Uhudu, a kan musulmi, haka yay akin Ahzab, bai gushe ba tyana adawa da musulunci har zuwa kokacinda manzon All..(s) ya yi masu ba zata a fatahin makka, aka kama abu sufyan aka zo da shi gaban manzon All..(s). An ce mai ya musulunta ko a katse wuyarsa, sai ya ki, sai da ya ga ba makawa sai ya amince da da cewa babu abin bauta da gaskiya sai All.., amma yaki ya shaida muhammadu manzon All..(s) ne, shi ma sai da ya ga ba makawa sai yace to ya amince.
Don haka yana daga cikin mu’allafatu Kulubuhum, man zon All..ya bashi, rakumo 100 bayan yakin Husain, don kodaitar da shi yayi Imani.
Amma a lokacinda Uthman ya sami Khalifanci, ya bashi darhami, 200,000 daga baitul Mali.
An ruwaito cewa bayan da Uthman ya sami Khalifanci, sai Abusufyan ya je kan kabarin Hamza Ammin manzon All..(s) yana tattaka kabarin, yana cewa ya Aba Ammarah abinda kuka zare takobi a kammu domin shi a jiya ya koma hannun yayammu suna wasa da ita.
Sannan wata rana ya shiga wajen Uthman bayan ya makanace, sai ya tambaya, ba kowa sai mu sai ake ce masa, ee, sai yak u Bani Umayya ku yi ta jujjuyata a tsakaninku, ba rantse da abinda Abusufyan yake rantsewa da shi babu wata Aljanna ko wuta. Abu sufyan ya dauki shekaru kimani 20 yana kiyayya da addinin musulunci da manzon Al..(s) da iyalan gidansa, har fatahin Makka.
02- Harith dan Hakam, khalifa Uthman ya bashi dinari 300,000. Sannan an kawo rakuman zakka madina, ya bashi su gaba daya. Haritha dai surukinsa ne a kan diyarsa A’isha. Kuma dan amminsa ne. Zakka dai ta talakawam musulmi ne, amma ya bada shi ga makusantansa.
3-Abdullahi dan Sa’id an Abi sarkh, wanda ya bashi ganimar da aka sami a Afrika gaba daya, sannan ya sa shi gwamnan kasar Masar, Ganimar wanda aka samo daga Tarabulus da kuma Tanja daga arewacin Afirka.
Abdullahi dan sa’in dan Abisharkh yana daga cikin fitattu masu adawa da musuluinci a Jahiliyya,. Yana matukar kiyya da kuma aibata manzon All..(s). Har sai ya fadawa musulmi a fatahin Makka, duk wanda ya ga Abdullahi dan Abi sharkh ya kashe shi, ko da ya sameshi yana rike da Kellen Ka’aba ne. yana daga cikin wadanda suka shiga musulunci bayan an sami nasara a kansu a fatahin makka.
4-Hakam dan Abi Ass, shi ma yana daga cikin wadanda suke adawa da musulunci, sannan bayan da addinin musulunci ya sami nasara, yana isgili da manzon All..(s) a Madina, yana koikoyonsa, sannan yana jujjuya bakinsa da fuskansa a bayan manzon All..(s) sai manzon All..(s) ya juya ya ganshi, sai y ace ka kasance haka, sai fuskansa ta turmude ta zama hakan har ya mutu a hakan.
Cutarsa ta kai ga manzon All..Ya la’aneshi da shi da zuriyyarsa sai muminin daga cikinsu. Sannan ya koreshi daga Madina, y ace ba zai zauna da shi a gari guda ba. Sai ya koma Ta’ifa da shi da yayansa.
Bayan wafatin manzon All..(s) Uthman ya bukaci Khalifa Abubakar da Khalifa Umar su dawo da shi madina, sun ki sun ce ba zasu dawo da wannan manzon All..(s) ya kora daga madina ba.
Amma uthman yana hawa, ya dawo daga. Wasu sun bayyana cewa sun gan shi a lokacinda ya dawo madina yana cikin wani hali na talauci, amma da ya shiga wajen Uthman kawai sai ya fita da Jabba. Tu banda haka Khalifa Uthman ya bashi kudaden Jama’a wanda ya kai dinari 100,000.
Sannan ya bashi aikin karban zakka, a wani wuri, ya tara dirani 300,000 Khalifa ya bashi su gaba daya.
05-Sannan Khalifa ya bawa Sa’id dan Ass dinari dubu 100. Shi ma ya shahara da kiyayya da addini da kuma. Babansa ya mutu a Badar a hannun Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a). Yana kasance fasiki cikin fasikan baunu umayya.
06- Walid dan Ukba, dan uwan khalifa Uthman ta mahaifiyansa. Wanda ya aikashi a matsayin wali a Kufa, sai ya karbi bashi daga ma’ajin baitul malin musulmi a lokacin wanda shi ne, Abdullahi dan Masa’ud. Sai dan Masa’ud ya tambaye shi kudadeb bashin da ya karba, sai Walid ya rubutawa Khalifa ya fada masa abinda Abdullahi dan masa’ud yake masa. Sai Khalifa ya rubutawa Abdullahi dan Masa’ud y ace masa, kai mai ajiya ne, amma ba ruwanka da yadda za’a kashe kudaden.
A lokacinda Abdullahi dan masa’ud ya karanta wasikar khalifa, sai ya je ya jefawa Walid makullin baitul mali, sai ya ce masa. Ni ina tsammanin ina tsaron dukiyar musulmini, idan ku nake tsarewa dukiyar ba zan yi aikin ba. Sai ya kama hanyarsa ya dawo madini.
07-Marwan da Hakam, wanda yake tsotson babansa Hakam a lokacin da manzon All..(s) ya la’aneshi. Bayan da Khalifa Uthman ya dawo dasu Madina, ya mika masa baitul malin musulmi yana bawa wanda ya ga dama ya hana wanda ya ga dama.
Marwan ya kasance shugaban daga cikin munafukai, Imam Ali(a) ya ganshi sai yace: Kaitonka, kuma bune ya tabbata ga al-ummar Mohammadu daga sharrinka, daga kuma sharrin gidanka, …).
Khalifa Uthman ya bawa Marwan Khumusin ganimar arewacin Afirka. Wanda ya kai dinari 500,000.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: khalifa Uthman ya Khalifa Uthman ya yana daga cikin wadanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Bindiga A Ƙarƙashin Jagorancin Turji Sun Kashe Manoma 12 A Sokoto
Ya ce, “Akwai rahoton cewa Turji ya shirya zai ziyarci yankin Gabashin Gatawa domin gudanar da bukukuwan Sallah, amma matakin da jama’a suka dauka na sanar da jami’an tsaro ya dakatar da shi ga hakan.
“Wannan na iya zama dalilin da ya sa Bello Turji ya huce fushinsa a kan manoman da ba su ji ba gani ba.”
Sai dai hukumomin ‘yansanda a jihar sun ki cewa komai kan lamarin.
Majiyar ‘yansandan ta yi ikirarin cewa, “tunda ana ci gaba da aikin hadin gwiwa na sojoji a yankin, ‘yansanda ba su da hurumin yin magana kan ci gaban tsaro a yankin.
Da aka tuntubi runduna ta 8 ta sojojin Nijeriya ta mika wakilinmu ga rundunar ‘Operation FASAN YAMMA’, wanda har yanzu bai amsa bukatar wakilinmu ba kan bukatar tabbatar da lamarin harin har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp