Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta
Published: 6th, April 2025 GMT
Ta kuma bukaci Amurka da ta daina amfani da harajin fito a matsayin makami don dakile ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da kuma tauye hakkin samun halaltacciyar ci gaba na al’ummar Sinawa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku.
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Za Ta Kara Sanya Harajin Fito Na Kaso 34% Kan Dukkan Kayayyakin Da Take Shigowa Daga Amurka
Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun hakkoki da muradun kasashe mambobin WTO, kuma ya matukar dagula ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da kuma tsarin tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa.
Bugu da kari, hukumar harajin kwastam ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, kasar Sin za ta kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, farawa daga ranar 10 ga watan Afrilun nan da muke ciki. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp