Aminiya:
2025-04-26@22:14:48 GMT

An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe

Published: 6th, April 2025 GMT

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan wata motar bas ta sufurin fasinja ta Benue Links da ke kan hanyarta a titin Ikobi na ƙaramar hukumar Otukpo a Jihar Benuwe, inda suka kashe direban da wani fasinja na gaba, yayin da suka yi awon gaba da wasu fasinjojin.

Lamarin ya afku ne da yammacin ranar Alhamis a kusa da rusasshen kamfanin Benue Burnt Bricks, wanda aka fi sani da hanyar shiga garin Otukpo.

’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi Motar fasinja ta kama wuta wasu sun tsallake rijiya da baya

Motar mallakar gwamnatin Jihar ta kamfanin Benue Links Nigeria Limited tana kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo lokacin da aka yi mata kwanton ɓauna.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na kamfanin, Johnson Ehi Daniel ya fitar a ranar Juma’a, ya tabbatar da faruwar harin, ya kuma yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa, tare da bayyana ƙwarin gwiwar ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da fasinjojin da aka sace.

“Benue Links Nigeria Limited ta yi takaicin sanar da harin da aka kai kan wata motar safa mai lamba PP512. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, kusa da Otukpo Burnt Bricks lokacin da wasu mahara ɗauke da makamai suka yi wa motar kwanton ɓauna.

“Abin takaici, maharan sun harbe direban motar bas mai kujeru 18, Mista Samuel Agege da wani fasinja na gaba, yayin da ’yan bindigar suka yi yunƙurin sace sauran fasinjojin, wasu mutane uku sun yi nasarar tserewa, wani kuma ya sauka tun da farko a garin Taraku kafin faruwar lamarin,” in ji sanarwar.

Hukumomin kamfanin sufurin sun jajantawa iyalan waɗanda suka rasu tare da yin alƙawarin ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro domin ganin an dawo da fasinjojin da aka sace.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: garkuwa da fasinjoji Jihar Benuwe

এছাড়াও পড়ুন:

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan kasar Labanon da Siriya yana da matukar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da ayyukan wuce gona da iri da na ta’addancin yahudawan sahayoniyya a Gaza da Lebanon.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Boko Haram Sun Kashe Mutum 12 A Wani Sabon Hari A Borno
  • Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina  Cikin Masifar Yunwa
  • Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Yi Gargadin Munanan Sakamakon Da Zai Biyo Bayan Kashe Falasdinawa
  • An kashe Shugaban coci da wata mace a Benuwe
  • An sako limamin Katolika da aka sace a Kaduna
  • ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa 
  • Mutum 7 Sun Shiga Hannu Kan Zargin Fyaɗe Da Kashe Budurwa A Bauchi
  • An kama wasu mata na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace
  • ‘Yan Tawayen Sudan Sun Kashe Fararen Hula 47 A Birnin El-Fasher Fadar Mulkin Darfur Ta Arewa
  • Jiragen yakin Amurka sun kara kai hari kan kasar Yemen