Rashin ɗa’a: Gwamnatin Borno ta gargaɗi masu amfani da shafukan sada zumunta
Published: 6th, April 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman A.
Inda ta yi nuni da cewa, waɗannan kalaman sun saɓawa al’adunmu da tsarin rayuwarmu, musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo da ke nuna yadda matasa ke caccakar manyan jami’an gwamnati da munanan kalaman cin zarafi da cin mutuncin tare da ƙalubalantar manufofin gwamnati ba tare da cizawa su hura ba.
A cewar sanarwar wannan halayya da waɗannan matasa ke nunawa abin tur ne kuma ba abin yarda ba ne.
Don haka gwamnatin jihar tana kira ga matasanta da su kiyaye da ɗabi’un da ba su dace da al’adunmu ba.
Sanarwar ta kuma jaddada sunan jihar a matsayin ‘Gidan Zaman Lafiya’, tare da bayyana muhimmancin kiyaye zaman lafiya da juna a tsakanin al’ummominta daban-dabam.
Yayin da take amincewa da ’yancin faɗin albarkacin baki, da gudanar da taro cikin lumana da tsarin mulki ya ba su, gwamnati ta bayyana ƙarara cewa ba za ta amince da keta doka da oda ko kuma keta kundin tsarin mulki ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ƙofofin gwamnati a buɗe suke a kodayaushe don bayyana koke-koke na jama’a yadda ya kamata da kuma aiki mai ma’ana,” in ji sanarwar.
“Duk mai son bayyana ra’ayinsa, to ya yi hakan amma bisa manufa ta doka, kuma ’yan ƙasa su guji yin kalamai marasa daɗi kana a guji yaɗa labaran ƙarya ko nuna ƙyama domin duk wanda ya karya doka zai fuskanci fushin hukuma.’
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kafafen sada zumunta na yanar gizo
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta Bayyana cewa: TattaunawarMuscat Wata Dama Ce Ta Samun Zaman Lafiya Kan Batutuwan Masu Sarkakiya
Mai ba da shawara ga Jagoran juya juya halin Musulunci kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Tattaunawar Muscat wata dama ce ta samun zaman lafiya kan batutuwa masu sarkakiya
Ali Shamkhani mai ba Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin siyasa ya yi tsokaci kan tattaunawar ba na kai tsaye ba da ake yi tsakanin Iran da Amurka a babban birnin kasar Omani na Muscat.
A cikin jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na twitter, Shamkhani ya bayyana cewa: Fiye da kwanaki 100 ke nan da Trump ya hau kan karagar mulki, yana mai cewa: “Ba a warware manyan batutuwan da suka shafi Yemen, Gaza, Ukraine, da rikicin haraji ba, baya ga gibin kasafin kudi, har yanzu ba a warware ba.”
Ya ci gaba da cewa: “A cikin wannan yanayi, tattaunawar Muscat ta bayyana a matsayin wata dama ta samun nasara ta hadin gwiwa tsakanin bangarorin da abin ya shafa (Amurka da Iran).”
Shamkhani ya kammala rubutunsa a twitter da cewa: Wadannan shawarwarin sun ginu ne a kan manyan ka’idoji guda uku: gaskiya (wanda ke tabbatar da cewa babu wata karkata daga manufofin da aka sa gaba); Ma’auni (wanda ke buƙatar ɗaga duk takunkumin da aka sanya); Da kuma bin doka (wanda ke ba da tabbacin haƙƙin haɓakawa cikin tsarin dokokin ƙasa da ƙasa).