Amurka ta soke duk wata takardar izinin shiga kasar da aka baiwa ‘yan Sudan ta Kudu
Published: 6th, April 2025 GMT
Amurka ta sanar da soke duk wata takardar izinin shiga kasar wato (visa) da kasar ta baiwa duk wani dan Sudan ta Kudu.
Matakin a cewar Amurka na da nasaba ne da yadda Sudan ta Kudun ta ki karbar ‘yan kasarta da aka kora daga kasar.
A cikin wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya fitar, ya ce ‘’ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta soke duk bizar kasar da ‘yan Sudan ta Kudu ke rike da a nan take.
Wannan shi ne irin matakin farko da aka dauka kan wasu ‘yan kasa a duniya tun bayan da Donald Trump ya koma kan karagar mulki a ranar 20 ga watan Janairu, a tsauraran manufofinsa na yaki da bakin haure.
Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya kara da cewa lokaci ya yi da gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta Kudu za ta daina samun wani tagomashi daga Amurka.
Kaddamar da dokar ta shige da fice na kasarmu yana da matukar mahimmanci ga tsaron kasa da amincin jama’a na Amurka.
Dole ne kowace kasa ta amince ta karbi yan kasarta da aka kora nan da nan inji gwamnatin ta Amurka inji shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Azerbaijan Ya Tattauna Da Wakiliyar CMG
Kwanan nan, wakiliyar CMG ta zanta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev wanda ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin zantawar, shugaba Aliyev ya waiwayi dadadden tarihin cudanyar kasashen biyu da ma zumuncin da ke tsakaninsu, kuma ya yi imanin da cewa, kasancewar dukkansu kasashe masu tasowa ne, kasashen biyu za su hada hannu wajen bayar da karin gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya.
Shugaba Aliyev ya ce, “Muna ganin kasar Sin jagora ce ga kasashe masu tasowa na duniya, kuma tana taka rawar gani a wajen hada kan kasa da kasa, musamman ma wajen yayata ruhin Bangdun, ciki har da martaba ikon mulki da cikakkun yankunan kasa na sauran kasashe, da rashin tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe, da kiyaye zaman daidaito da cudanyar bangarori daban daban, da nuna kin yarda da babakere da sauran danniya a duniya daga kowace kasa ko kungiya.”(Lubabatu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp