Red Crescent ta Falasdinu ta nemi a yi bincike kan kisan da Isra’ila ta yi wa ma’aikatan agaji
Published: 6th, April 2025 GMT
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan da Isra’ila ta yi wa ma’aikatan agaji a zirin Gaza, bayan da wasu sabbin hujjojin bidiyo suka nuna yadda sojojin Isra’ila suke harbin motocin daukar marasa lafiya.
Bidiyon da ya ci karo da wani nau’in lamarin da sojojin Isra’ila suka yi cewa “an gano wasu motoci marasa da yawa suna tunkarar sojojin Isra’ila ba tare da fitillu ko alamun motocin ambullance na gaggawa ba”.
Shugaban kungiyar agajin ta Falasdinu Younes al-Khatib, ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kashe-kashen, yana mai jaddada cewa ba za a iya amincewa da binciken da sojojin Isra’ila ke jagoranta ba.
“Ba mu amince da duk wani binciken da sojojin suka yi ba, kuma wannan ne ya sa muka fito fili a kan cewa muna bukatar bincike mai zaman kansa kan lamarin,” in ji al-Khatib a wani taron manema labarai a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York, yayin da yake magana kan harin da ya kashe likitoci da ma’aikatan jin kai 15 a Gaza.
Ya yi Allah wadai da karuwar hare-haren da ake kai wa ma’aikatan jin kai da wuraren aikinsu, yana mai jaddada cewa ana kai hari kan tambarin kungiyar agaji ta Red Crescent, wanda ya kamata a kiyaye a karkashin dokokin kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sojojin Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
Mahaifi ya kashe ɗansa mai shekara 6 don yin tsafi a Gombe
Wani mummunan al’amari ya girgiza al’umma a Ƙaramar Hukumar Kwami, Jihar Gombe, inda ake zargin wani magidanci ya jagoranci sacewa da kashe ɗansa mai shekara shida domin yin tsafin kuɗi.
Ana zargin cewa mahaifin yaron shi ne jagoran kisan kuma Yana cikin waɗanda suka tsere, a yayin da hukumomi ke ci gaba da farautar sa.
Tuni ’yan sanda suka cafke mutane takwas bisa zargin wannan aika-aika a unguwar Bura-Bunga da ke ƙaramar hukumar.
Kakakin ’yan sanda a Jihar Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya sanar cewa waɗanda suka shiga hannu sun amsa cewa sun kashe yaron ne bisa umarnin bokaye da suka nemi sassan jikin ɗan Adam don yin tsafin kuɗi.
An kama mutane 13 kan zubar da ciki a Bauchi ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a NasarawaBincike ya nuna wani mai shekaru 45, wanda ake zargin shi ne shugaban gungun, ya hallaka yaron tare da raba sassan jikinsa gida biyu.
Ɓangaren sama na jikinsa an jefa shi cikin rijiyar, yayin da ɓangaren kasa aka bai wa abokan laifinsa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu bokaye biyu ne suka nemi sassan jikin yaron, kuma wani matashi mai shekaru 18 ne ya sace yaron, sannan wani ya haɗa bokayen da su.
Kwamishinan ’yan sanda, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa za a tabbatar an gurfanar da duk masu hannu a wannan mummunan kisa a gaban ƙuliya.
Ya kuma yi kira ga jama’a su riƙa sa ido tare da bayar da rahoto kan duk wani abu mai kama da waɗanda ake nema jami’an tsaro.
Rundunar ’yan sanda ta jaddada aniyarta na kawo ƙarshen irin waɗannan munanan laifuka a faɗin jihar ta Gombe.