An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36
Published: 6th, April 2025 GMT
Da farko Kinjal Lathi, ta fara cire rai daga samun haihuwa da jin daɗin zama a matsayin uwa saboda cutar borin jini ta thalassemia da take fama da ita.
Dole a riƙa yi mata mata ƙarin jini duk bayan mako biyu, sannan dole ta bi wasu ƙa’idojin cin abinci da magunguna.
Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya (2) ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyiBayan kuma cutar da take fama da ita, akwai kuma ƙalubalen ɗaukar ciki da take fama da shi.
‘’Ina ganin fuskar ’yata sai na manta da duk wata wahalar da na sha a sanadiyar ɗaukar ciki da naƙudar,” in ji Kinjal Lathi, daga yankin Ahmedabad da ke Jihar Gujarat a kasar Indiya, inda ta ƙara da cewa, “ni da mijina mun sha kuka.”
“Akwai barazana babba ga uwa da abin da ke cikinta. Amma na yanke shawarar cika burina na zama uwa,” in ji Kinjal, kamar yadda majiyar BBC ta ruwaito.
Sai dai an yi wa Kinjal ƙarin jini sau 36 lokacin da take da ciki, amma kuma ta haifi lafiyayyiyar jaririya a ranar 12 ga watan Yulin 2019.
Ko bayan haihuwar ma, sai da aka ci gaba da yi wa Kinjal mai shekara 25 ƙarin jini, inda ta ce wasu lokutan ma ana yi mata ƙarin jinin ne a yayin da take shayar da jaririyarta.
Sannan kuma wani abun farin cikin shi ne ’yarta ba ta gaji cutar ba.
Wata ƙwayar halitta ce take samun matsala, wadda ke hana cuɗanyar jini da iska domin samar da jinin da ake kira haemoglobin, wanda shi ne yake zagayawa da jini mai ɗauke da sinadarin protein a jiki.
Yaya cutar thalassemia ke shafar juna biyu?
Ba a cika masu irin wannan cuta irin Kinjal suna haihuwa lafiya ba, kamar yadda likitan yara, Anil Khatri, wanda yake cikin kwamitin kar ta kwana na yaƙi da cutar ya bayyana.
Ya ce, bai taɓa ganin haka ba sama da shekara 30 da ya yi yana aikin kula da masu cutar ba, inda ya yi jinyar masu cutar sama da guda 100.
Akwai masu cutar kusan miliyan 270 a duniya, kamar yadda ma’aikatar lafiya da walwalar iyali ta bayyana.
Akwai na’ukan cutar da dama, ciki har da wadda ake kira ‘Hemoglobin H disease’, wadda ita ma ta kasu kashi biyu, wato nau’in alpha da beta – nau’in beta (TM) ce ta fi illa.
A Indiya akwai yara kimanin 100,000 zuwa 150,000 da suke ɗauke da cutar.
Ɗaukar ciki abu ne mai wahala ga mata masu cutar, kamar yadda likitan haihuwa, Umar Khatri ya bayyana.
Idan mace na da juna biyu, jininta yana ƙaruwa, wanda hakan ya sa jikin ke buƙatar ƙarin sinadarin ‘iron’ domin tallafa wa kai iska zuwa ga jariri.
“A ƙa’ida muna kiran mata masu juna biyu ne, su zo a duba su aƙalla sau ɗaya a wata.
“Amma ita Kinjal tana zuwa ne duk kwana 15, wanda shi ne karo na farko da muka samu hakan,” in ji Khatri.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Indiya ƙarin jini ƙarin jini kamar yadda
এছাড়াও পড়ুন:
An kama wasu mata na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace
Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7.
An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi.
An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojojiWaɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin Zamba da ke Abuja, yayin da ta ukun da ake zargin ma’aikaciyar jinya ce da ta tsere a yanzu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Henry Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
Okoye ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a Owerri, babban birnin jihar a ranar 14 ga watan Afrilu, biyo bayan wani samame da jami’an tsaro suka yi a lokacin da suke ƙoƙarin siyar da yaron kan kuɗi Naira miliyan 2.7.
Ya ce, an kama mutanen ne biyo bayan ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin rundunar ’yan sandan Jihar Imo da hedikwatar ’yan sandan shiyya ta 7 da ke Abuja, duk da cewa an miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na shiyyar Abuja, domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.
Okoye ya ce, “Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta gano wani mutum da ake zargi da safarar ƙananan yara, lamarin da ya kai ga cafke wasu mata biyu da ake zargi tare da kuɓutar da wani yaro ɗan shekara huɗu.