Yadda Amarya Za Ta Gyara Jikinta Har Zuwa Ranar Aure (II)
Published: 6th, April 2025 GMT
(3).sinadare gyaran jiki: to anan fa matsalar take don gaskiya awannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kinsha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda anfison aga amarya acike baza ki gane dagaske nake ba sai kin zauna nan awaje namiji yagama tsaraki yana ce miki kin hadu kina jin kanki kawai sai ranar daran farko za ki fara ganin canji.
Saboda haka koda bayanshi ma akwai wasu supplement dazasu kara miki kyau lokacin aurenki yakamata kinemo asalin original kisha domin yawancin mata dakike ganin jikinsu sumul sumul kamar su sukayi kansu ki gansu kamar alashe yanzu duk su suke sha shikuma gaskiya beda wata matsala da yawa domin suna kokari wurin inganta shi sosai.
Zamu ci gaba mako mai zuwa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Amarya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudin al’umma ba ga mutanen da ba za su iya kula da mahajjata yadda ya kamata ba.
Gwamna Radda ya kara da cewa ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi guda 34 domin tabbatar da cewa malaman da suka cancanta ne kadai aka zaba a matsayin masu koyarwa a ayyukan aikin hajjin bana.
Ya kuma yi alkawarin kafa kwamitin yada labarai domin yada ayyukan aikin hajjin tare da ba da kulawa ta musaman kan shawarwarin da aka bayar kan rahoton da kwamitin aiki hajjin ya gabatar.
Da yake gabatar da rahoton, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Katsina kuma Amirul Hajj, Alhaji Tukur, ya bayyana wasu muhimman batutuwa da ke bukatar kulawa.
Ya kuma bayyana bukatar tallafa wa hukumar kula jin dadin alhazai wurin tantance malamai. Yana mai cewa mafi yawancin shugabannin kananan hukumomi sun sanya malaman da ba su da kwarewar yadda za su koyar da mahajjatan.
Amirul Hajja ya nuna damuwarsa bisa yadda ake samu wadanda ba ‘yan Nijeriya ba a cikin mahajjatan jihar tare da ba da shawarar inganta hanyoyin da ake bi wurin tantance mahajjatan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp