Aminiya:
2025-04-07@09:57:14 GMT

De Bruyne zai yi bankwana da Manchester City a ƙarshen kaka

Published: 6th, April 2025 GMT

Ɗan wasan ƙasar Belgium, Kevin De Bruyne, ya sanar da cewa zai yi bankwana da ƙungiyar Manchester City ta Ingila a ƙarshen kakar bana.

Fitaccen ɗan wasan tsakiyar mai shekaru 33 ya sanar da hakan ne cikin wata saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X.

Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu

De Bruyne ɗan asalin ƙasar Belgium ya tabbatar da cewa waɗannan su ne watanninsa na ƙarshe a matsayin ɗan wasan Manchester City.

De Bruyne ya je Manchester City a shekarar 2015 daga Wolfsburg, inda ya lashe duka manyan gasar ƙwallon ƙafa tare da ƙungiyar ta City, ciki har da gasar Firimiya ta Ingila da Gasar Zakarun Turai.

Kwantaraginsa a City zai ƙare a ƙarshen Yunin bana, amma har yanzu ba a tabbatar ko zai haska ba a wasannin da City za ta buga daga 14 ga Yuni zuwa 13 ga Yuli.

“Kowane labari yana zuwa ƙarshe, amma lallai wannan ya kasance babi mafi kyau a gare ni.

“Mu mori waɗannan lokutan tare har zuwa ƙarshe,” a cewarsa.

De Bruyne ya buga wasanni 280 a gasar Firimiya, kuma ya ci ƙwallaye 70 da tallafin ƙwallaye 118.

Hakan ya sa shi yake biye da Ryan Giggs tsohon ɗan wasan Manchester United, wanda yake riƙe da kambun wanda ya fi ba da tallafin cin ƙwallo a tarihin Firimiya, da ƙwallaye 162.

 

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Amarya Za Ta Gyara Jikinta Har Zuwa Ranar Aure (II)

(3).sinadare gyaran jiki: to anan fa matsalar take don gaskiya awannan yanayin idan har kina so ki ga kyakkyawan sakamako dole sai kinsha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda anfison aga amarya acike baza ki gane dagaske nake ba sai kin zauna nan awaje namiji yagama tsaraki yana ce miki kin hadu kina jin kanki kawai sai ranar daran farko za ki fara ganin canji.

Saboda haka koda bayanshi ma akwai wasu supplement dazasu kara miki kyau lokacin aurenki yakamata kinemo asalin original kisha domin yawancin mata dakike ganin jikinsu sumul sumul kamar su sukayi kansu ki gansu kamar alashe yanzu duk su suke sha shikuma gaskiya beda wata matsala da yawa domin suna kokari wurin inganta shi sosai.

Zamu ci gaba mako mai zuwa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fulham ta doke Liverpool bayan wasa 26 a jere ba tare da rashin nasara ba
  • ACF ta nemi Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen kisan jama’a a Filato
  • Southampton Ta Koma Rukunin Ƴan Dagaji Bayan Shan Kashi A Hannun Tottenham
  • Yau Ta Ke Manchester Dabi 
  • Yadda Amarya Za Ta Gyara Jikinta Har Zuwa Ranar Aure (II)
  • Kofin Duniya: Kocin Nijeriya Na Fatan Matashin Ɗan Wasan Arsenal Nwaneri Ya Wakilci Ƙasar
  • Bruno Fernandes Ba Na Sayarwa Ba Ne – Ruben Amorim
  •  Falasdinawa 86 Ne Su Ka Yi Shahada A Cikin Sa’o’i 24 Da Su Ka Gabata
  • De Bruyne Zai Bar Manchester City A Ƙarshen Kakar Wasanni