HausaTv:
2025-04-07@11:42:37 GMT

Ana Ci Gaba Da Kai Ruwa Rana Takanin Amurka Da China Kan Batun Harajin Fito

Published: 6th, April 2025 GMT

Gwamnatin kasar Sin ta yi kakkausar suka da bayyana adawarta ga matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya.”

A cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin na Amurka, wanda ya kasance daukar mataki bisa radin kai, da kuma kariyar cinikayya da cin zarafin tattalin arziki.

Sanarwar ta kara da cewa, ta hanyar fakewa da abin da take kira “ramuwar gayya” da “adalci,” a zahiri dai Amurka ta tsunduma a aiwatar da dabarun danniya da babakere, tana neman cimma manufarta ta “Amurka na gaba da komai” da kuma “Amurka ta fi kowace kasa.” Har ila yau, Amurka na amfani da harajin fito don kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, tare da fifita muradun Amurka sama da moriyar bai daya ta duniya, tare kuma da sadaukar da halaltattun muradun kasashen duniya don cimma burin Amurka.

A ranar Laraba ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da wani sabon tsarin haraji, inda ya sanya mafi kankantar harajin fito kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga dukkan kasashe abokan huldar cinikayyarta da kuma karin sama da hakan kan waasu kasashen. Bayan matakin na Amurka, a ranar Juma’a kasar Sin ta sanar da cewa, za ta sanya karin harajin fito kashi 34 cikin dari kan dukkan kayayyakin da ake shigowo da su daga Amurka daga ranar 10 ga watan Afrilu, wanda ya yi daidai da harajin fito na ramuwar gayya da Amurka ta kakaba kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin.

A cikin sanarwar da gwamnatin kasar Sin ta fitar yau Asabar ta ce, kasar Sin ta dauki kuma za ta ci gaba da daukar kwararan matakai don kiyaye ‘yancinta, da tsaro, da muradunta na samun ci gaba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Sin ta harajin fito

এছাড়াও পড়ুন:

Ƙarin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arziƙin Duniya

Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani.

Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu da kaso mai yawa, sakamakon karin kudaden hajojin da ake samarwa a masana’antun kasashen da Amurkan ta karawa haraji.

La’akari da wadannan illoli, kamata ya yi Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta dakatar da matakan kakaba haraji marasa ma’ana, kana ta koma teburin tattaunawa, domin warware duk wani savani na kasuwanci da cinikayya tare da dukkanin sassan da batun ya shafa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Guteress : ba wadan zai ci ribar yakin cinikayya
  • Me Yakin Harajin Fito Zai Haifar Wa Amurka?
  • Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Amurka Da Jakadan Sin A Burtaniya Sun Nuna Adawa Da Matakin Harajin Fito Na Ramuwar Gayya Da Amurka Ta Dauka
  • Ƙarin Harajin Amurka Zai Illata Tattalin Arziƙin Duniya
  • Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO
  • China Za Ta Kara Harajin Fito Da Kashi 34% Kan Kayayyakin Da Take Shigo Da Su Daga Amurka
  • Kasar Sin Za Ta Kara Sanya Harajin Fito Na Kaso 34% Kan Dukkan Kayayyakin Da Take Shigowa Daga Amurka
  • Manyan Cibiyoyin Kudi Na Duniya Sun Yi Gargadai Akan Sabbin Kudaden Fito Na Amurka
  • Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Matakan Harajin Fito Na Amurka Sun Sa Ta Zama Makiyiyar Duniya